Yan Bindiga Sun Tarwatsa Mutane a Jihar Taraba, Sun Sace Wasu Da Dama

Yan Bindiga Sun Tarwatsa Mutane a Jihar Taraba, Sun Sace Wasu Da Dama

  • 'Yan bindiga sun tashi mutane a garuruwa sama da 15 a yankin ƙaramar hukumar Bali da ke jihar Taraba
  • Mazauna garuruwan da abun ya shafa sun bayyana cewa maharan sun sace mutane da yawa a harin wanda ya ɗauki lokaci mai tsayi
  • Kakakin hukumar 'yan sanda, SP Usman Abdullahi, ya ce rahoton da ya riske su ya nuna mutane 14 aka sace

Jihar Taraba - Wasu ‘yan bindiga da suka kai farmaki yankin Garba-Chede da ke karamar hukumar Bali a jihar Taraba sun yi garkuwa da mutane da dama da suka hada da mata da ƙananan yara.

Daily Trust ta tattaro cewa ‘yan bindigan masu yawa sun shiga garuruwan da lamarin ya shafa a daren Lahadi, inda suka tilasta wa mazauna yankin tserewa daga gidajensu a harin wanda ya dauki tsawon sa’o’i.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Kama Jami'an Gwamnati Da Ke Karkatar da Tallafin da Ake Raba Wa Talakawa

Harin 'yan bindiga a jihar Taraba.
Yan Bindiga Sun Tarwatsa Mutane a Jihar Taraba, Sun Sace Wasu Da Dama Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Wasu daga cikin ƙauyukan da harin yan bindigan ya shafa sun hada da Garbatau, Mirimidankol, Gidan Hamidu, Dangiwa, Nayinawa, Garin Gima, Bantaguru, ShaDussa, Garin Bose, Mailabari, da sauransu.

Halin da mutane suka shiga

Wani mazauni, Ali Dauda Garba-Chede ya cw ɗaruruwan ‘yan gudun hijira da suka hada da mata da kananan yara sun gudu zuwa garin Garba-Chede daga kauyukan da ‘yan bindigan suka tarwatsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce har yanzu jami’an tsaro ba su kai ɗauki ba, inda ya ce mafarauta da ’yan banga da suka kai ɗauki, sun gudu saboda ba za su iya tunkarar maharan ba.

Wasu daga cikin mutanen da suka tsere zuwa Garba-Chede sun ce ‘yan bindiga a kan babura sun bi kauye zuwa kauye suna sace mutane tare da shanun jama'a.

Ya ce sama da garuruwa 15 ne suka tarwatse sakamakon harin 'yan bindigan daji. Mutumin ya ci gaba da cewa:

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Miyagun 'Yan Fashi Sun Kai Kazamin Hari Yankuna Uku a Babban Birnin Jihar PDP

"Yan bindigan suna da yawa kuma ɗauke da manyan makamai, sun shigo a kan Babura kowane Babur na ɗauke da mutum biyu zuwa uku."

Hukumar 'yan sanda ta tabbatar da lamarin

Mai magana da yawun hukumar 'yan sanda reshen jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, ya tabbatar da kai harin amma ya ce mutane 14 kaɗai aka sace, Dailypost ta tattaro.

Gwamnatin Zamfara Ta Sanar Da Rufe Wasu Kasuwanni a Kananan Hukumomi 5

A wani labarin kuma Gwamnatin Zamfara ta rufe wasu kasuwannin dabbobi a ƙananan hukumomi biyar na jihar sabida matsalar tsaro.

Kwamishinan yaɗa labarai da al'adu na jihar Zamfara, Mannir Mu’azu Haidara ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262