Mutane Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Kai Sabon Hari A Jihar Kaduna

Mutane Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Kai Sabon Hari A Jihar Kaduna

  • 'Yan bindiga sun kai sabon kazamin harin kan mutane a ƙauyen Dogon Noma-Unguwan da ke karamar hukumar Kajuru a Kaduna
  • Bayanai sun nuna maharan sun halaka mutane biyu kuma sun yi garkuwa da wasu mutum uku yayin harin na ranar Jumu'a
  • Har yanzu ba bu sanarwa a hukumance daga rundunar 'yan sanda reshen jihar ko gwamnatin Malam Uba Sani

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Miyagun 'yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 2 yayin da suka kai sabon mummunan hari ƙauyen Dogon Noma-Unguwan da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Channels tv ta tattaro cewa bayan kashe aƙalla rayuka biyu, 'yan bindigan sun kuma yi awon gaba da wasu mutun uku zuwa cikin daji.

Yan bindiga sun kai sabon hari a Kaduna.
Mutane Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Kai Sabon Hari A Jihar Kaduna Hoto: channelstv
Asali: UGC

Har yanzu hukumar yan sanda reshen jihar Kaduna ba ta fitar da sanarwa a hukumance kan sabon harin na safiyar Jumu'a ba.

Kara karanta wannan

Jimami Yayin Da 'Yan Bindiga Su Ka Sace Fitaccen Malamin Addini Da Wasu Mutum 2 A Jihar Arewa

Yadda maharan suka kashe mutum 2

Wani shugaban al'umma a garin Kufana, Musa Yaro, ya shaida wa manema labarai cewa 'yan bindigan sun shiga ƙauyen da safe, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce yayin haka suka bindige mutum biyu har lahira sannan kuma suka yi garkuwa da mutane uku, Daily Trust ta rahoto.

A cewar majiyar, sunayen wadanda aka kashe su ne Bala Laya da Gimbiya Coaster yayin da wadanda aka sace suka haɗa da Alkali, Mai Ceto Christopher da Sico Nicholas.

Ana yawan samun labarai marasa daɗi daga karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna sakamakon taɓarɓarewar tsaro da kai hare-haren 'yan bindiga.

Ɗaya daga cikin irin munanan hare-haren da yan bindiga suka kai yankin shi ne wanda ya faru ranar 11 ga watan Maris, 2019, inda mutane 52 suka mutu.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malamin Addini Da Wasu Mutum 3 a Wata Jihar Arewa

A wancan lokaci, harin ya kuma yi sanadin ƙona gidaje sama da 200 yayin da ɗaruruwan mutane suka gudu suka bar gidajensu saboda tsoron harin 'yan bindiga.

Hawaye Yayin da Wani Harsashi Ya Halaka Dalibar UNIZIK a Jihar Anambra

A wani labarin na daban kun ji cewa Wata ɗaliba da ke matakin shekarar farko a jami'ar Nnamdi Azikiwe (UNIZIK) Awka, ta rasa rayuwarta ba zato ba tsammani.

Ɗalibar ta mutu sakamakon wani harsashi da same ta wanda ake zargin 'yan kungiyoyin asiri ne suka harbo shi da yammacin ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262