'Yan Bindiga Sun Kai Hari Fadar Basarake, Sun Kashe Mai Neman Shiga Jami'a

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Fadar Basarake, Sun Kashe Mai Neman Shiga Jami'a

  • 'Yan bindiga sun kai farmaki fadar wani basarake, sun ƙona ɗalibi mai neman gurbin shiga jami'a a jihar Osun
  • Kawun wanda aka kashe ya bayyana cewa maharan sun ƙona gidan kafin daga bisani su kashe matashin ranar Lahadi
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta ce a halin yanzun kwamishina da wasu dakaru sun dira yankin domin kai ɗauki

Jihar Osun - Wasu ‘yan bindiga sun kai hari fadar Sarki a jihar Osun a ranar Lahadi, inda suka kashe wani mai neman shiga jami’a, Ibrahim Qudus, tare da kona gawarsa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa rikici ya ɓarke tsakanin al'ummomin ƙauyukan Ifon da Ilobu sakamakon sa'insar da ta shiga tsakani kan wani fili.

Yan bindiga sun kai hari fada a Osun.
'Yan Bindiga Sun Kai Hari Fadar Basarake, Sun Kashe Mai Neman Shiga Jami'a Hoto: punchng
Asali: Twitter

Kawun marigayin, Yarima Jimoh Qadri, wanda ya yi ikirarin cewa shi aka nufi kashewa, ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki gidansa da ke unguwar Okanla da safiyar Lahadi, suka buɗe wuta nan take.

Kara karanta wannan

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Kazamin Hari Cikin Jihar Kaduna, Sun Tafka Ta'adi

Yarima Gadri ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Na fita kenan da safiyar yau sai matata ta kira ni ta sanar da ni cewa wasu mutane kimanin 20 sanye da hula sun lulluɓe fuskokinsu sun shiga gidan ɗauke da bindigogi."
“Ban ajiye motata a waje ba don haka suka yi tunanin ina gidan mu da ke harabar Olokanla. Sun shiga suka bincika amma ba su same ni ba. Akwai mutum ɗaya da bai rufe fuska ba, sun lalata tagogin gidan."
"Na samu labarin sun gamu da wani kanina (Ibrahim Kudus) a gida, suka kashe shi tare da kone gidan. Bayan kashe yaron ne suka ja shi cikin mota suka kona shi a cikin motar."
“Kudus matashi ne dan shekara 28, yana neman admishin ɗin shiga jami'a. Ya zauna jarabawar UTME da ta gabata."

Wane mataki jami'an tsaron Najeriya suka ɗauka?

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Ɗalibar Jami'ar Tarayya Ta Mutu a Hanyar Zuwa Kasuwa

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar 'yan sanda reshen jihar Osun, Yemisi Opalola, ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce tuni aka tura jami'an 'yan sanda zuwa yankin.

A rahoton Daily Post, kakakin 'yan sandan ta ce:

"An ƙona wani mutumi a cikin mota a yankin Okanla, wanda ke tsakanin Ifon da Ilobu. Mun tura ƙarin dakaru domin daƙile abinda ka iya zuwa ya dawo, kwamishina da kansa ya na can."

APC Na Shirin Dakatar da Shugaban Jam'iyya a Jihar Ondo

A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC ta fara shirin ɗaukar tsattsauran mataki kan shugabanta wanda ya sa hannu aka lakaɗa wa kwamishinar mata duka.

A ranar Lahadi, wasu mutane suka zane kwamishinar mata yayin rabon kayan tallafi a karamar hukumar Akoko ta Arewa maso Yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel