Jami'an Tsaro da 'Yan Sa'kai Sun Halaka 'Yan Bindiga 21 a Jihar Kebbi

Jami'an Tsaro da 'Yan Sa'kai Sun Halaka 'Yan Bindiga 21 a Jihar Kebbi

  • Jami'an tsaron haɗin guiwa da mutanen gari sun halaka 'yan bindiga sama da 20 a yankin ƙaramar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi
  • Ciyaman ɗin yankin, Alhaji Hussani Aliyu-Bena ya tabbatar da haka, inda ya ce jami'an sun kuma ceto waɗanda aka yi garkuwa da su
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya ce har kawo yanzu rahoton faruwar lamarin bai riski hukumar ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kebbi - Jami'an tsaron haɗin guiwa da mambobin ƙungiyar 'yan sa'kai sun kashe 'yan bindiga aƙalla 21 a yankin ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi.

Shugaban ƙaramar hukumar Danko Wasagu, Alhaji Hussani Aliyu-Bena, shi ne ya tabbatar da haka ga wakilin Daily Trust, ya ce an samu wannan nasara ne ranar Laraba.

Jami'an tsaro sun ci nasara kan yan bindiga a Kebbi.
Jami'an Tsaro da 'Yan Sa'kai Sun Halaka 'Yan Bindiga 21 a Jihar Kebbi Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Ya ce ‘yan bindigar suna ƙoƙarin shiga Kebbi ne ta garin Mariga da ke Jihar Neja a lokacin gamayyar jami’an tsaro da ‘yan banga da ke yankin suka yi musu kwanton bauna a Tudun Bichi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Kammala Binciken Gawar Fitaccen Mawakin Nan Da Ka Tono Daga Ƙabari, Bayanai Sun Fito

Ya ce Wasagu ta haɗa boda da Mariga da ke jihar Neja kuma ta nan ne ‘yan fashin dajin watau 'yan bindiga ke samun saukin shiga ƙauyukan jihar Kebbi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ciyaman ɗin ya ce ‘yan bindigar sun kuma kashe Marafan Mai Inuwa a garin Kanya tare da yin awon gaba da wasu mutane da dama.

Amma a cewarsa daga bisani sojoji suka kubutar da su bayan sun kashe wasu daga cikin ‘yan bindigan a musayar wuta, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Ciyaman ya yaba wa jami'an tsaron

Shugaban ƙaramar hukumar ya jinjina wa jami'an tsaron haɗin guiwar da suka ƙunshi, sojoji, yan sanda, 'yan banga har da jama'an gari bisa namijin ƙoƙarin da suka yi.

Ya kuma yi kira ga mahukunta su ƙara tura Sojoji zuwa Malekachi da Dankade, ƙauyukan da yanzu suka zama hanyar 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Sanda Sun Tono Gawar Fitaccen Mawakin Nan Da Ya Mutu, Bayanai Sun Fito

A cewarsa, bisa umarnin Gwamna Nasiru Idris, tawagar gwamnatin ƙaramar hukumar sun ziyarci garin Kanya inda ‘yan gudun hijirar da suka baro ƙauyukan su suka taru.

Da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar, ya ce har yanzu hukumar ba ta samu rahoton abinda ya faru ba.

Yan Sanda Sun Kammala Bincike Kan Gawar Mawaki Mohbad a Jihar Legas

A wani rahoton kuma Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa an gama binciken gawar fitaccen mawakin nan Mohbad a jihar Legas.

Kakakin 'yan sanda na jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce a halin yanzun ana dakon sakamakon binciken gawar daga likitoci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel