Rundunar Soji Ta Yi Ajalin Babban Kwamandan Boko Haram, ArI Ghana A Jihar Borno

Rundunar Soji Ta Yi Ajalin Babban Kwamandan Boko Haram, ArI Ghana A Jihar Borno

  • Ana ci gaba da samun nasara kan ‘yan kungiyar Boko Haram yayin da sojoji su ka hallaka babban kwamnadansu
  • Rundunar ta hallaka babban kwamandan kungiyar mai suna Ari Ghana yayin wani kwantn bauna a Takaskala da ke Gwoza
  • Ari Ghana na daga cikin manyan masu fada aji na kungiyar musamman a yankin Dutsen Mandara da Ali Ngulde ke jagoranta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Borno – Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar sheke kwamandan ‘yan kungiyar Boko Haram, Ari Ghana a jihar Borno.

Rundunar ta bataliya ta 144 ta kuma kwamushe wasu da ke tsaron kwamandan guda biyar a Arewa maso Gabashin kasar.

Sojoji sun hallaka kwamandan Boko Haram, Ari Ghana
Rundunar Soji Ta Yi Ajalin Babban Kwamandan Boko Haram. Hoto: Nigerian Army.
Asali: Twitter

Yaushe sojojin su ka kashe Ari Ghana a Borno?

Kasurgumin kwamandan a kwanan nan ya kai mummunan hari kan rundunar soji da ke sintiri a kauyen Nvaha da ke kan hanyar Gwoza inda ya kashe sojoji da fasinja guda hudu.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Harbi Dalibai 3, Sun Sace Wata a Kwalejin Kimiyya a Wata Jihar Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar wa Zagazola Makama cewa sojoji sun yi artabu tare da kashe kwamnadan a Takaskala da ke karamar hukumar Gwoza a jihar Borno.

Majiyar ta ce:

“A ranar 25 ga watan Satumba, sojoji sun yi kwanton bauna a yankin Dutsen Mandara, bayan sa’a daya sai ‘yan Boko Haram su ka zo wucewa da babura.
“Yayin ganin ‘yan ta’addan, rundunar ta bude musu wuta inda ta hallaka ‘yan kungiyar biyar tare da Ari Ghana.”

Wane tasiri Ari Ghana ya ke da shi a Borno?

Kafin wannan lamari, Ari Ghanan shi ne na biyu a girma a wurin Ali Ngulde, shugaban kungiyar a yankin Dutsen Mandara inda ya jagoranci kai farmaki a yankunan Bama da Banki da Gwoza.

A farkon watan Satumba, Ari Ghana ya jagoranci wani mummunan hari tsakanin Banki da Darajamal inda su ka kashe sojoji da dama.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Yi Magana Mai Kyau Bayan Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Da Ya Samu a Zaɓen 2023

Mutuwar Ari Ghana ba karamar ci baya ba ne ga kungiyar ta Boko Haram wanda ya na daya daga cikin zaratan kungiyar, Leadership ta tattaro.

Majiya daga wani babban soja ta tabbatar cewa wannan na daga cikin nasarar da sojin ke samu kan ‘yan ta’addan a kwanakin nan.

'Yan Boko Haram sun hallaka mutane 4 har da soja 1

A wani labarin, 'yan kungiyar Boko Haram sun hallaka mutane hudu ciki har da wani soja a jihar Borno.

Wannan lamari ya faru ne a karamar hukumar Gwoza da ke cikin jihar inda su ka musu kwanton bauna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel