Akwai Alamun Tambaya Kan Wasu Yan Siyasa Game da Kashe-Kashen Filato, Mutfwang

Akwai Alamun Tambaya Kan Wasu Yan Siyasa Game da Kashe-Kashen Filato, Mutfwang

  • Gwamnan jihar Filato, Celeb Mutfwang, ya tona waɗanda yake zargi da hannu a ta'addancin da ake aikata wa a jiharsa
  • Ya ce akwai wasu 'yan siyasa da yake ganin ya kamata a titsiye su amsa tambayoyi kan alaƙarsu da 'yan ta'adda
  • A cewarsa suna amfani da halin da ake ciki a jihar Filato domin cimma wani muradinsu na siyasa

Jihar Filato - Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya ce wasu ‘yan siyasa na da tambayoyin da za su amsa dangane da kashe-kashen da ake yi a jihar.

Caleb Mutfwang ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa kan matsalar tsaron da ya addabi jiharsa a wata hira da gidan talabijin na Channels TV cikin shirin Politics Today.

Gwamnan jihar Filato, Celeb Mutfwang.
Akwai Alamun Tambaya Kan Wasu Yan Siyasa Game da Kashe-Kashen Filato, Mutfwang Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Ya yi bayanin cewa babu wata ƙabila da ke yaƙar abokiyar zamanta a jihar Filato, sai dai wasu bara gurbi da aka ɗauko haya domin su haɗa mutane faɗa su tada zaune tsaye.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da 'Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa da Babban Malami da Wasu 2 a Babban Birnin Jihar APC

A rahoton jaridar Daily Trust, Gwamna Mutfwang ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Babu wata kabila a jihar Filato da ke yaki da wata kabila, Abin da muke da shi a Filato ya wuce tunani a girman laifi."
"Asalin Abin da ke faruwa shi shi ne kisan kare dangi inda aka shigo da wasu bara gurbi daga waje domin su tada zaune tsaye, suna aikata ta'addanci a kan mutanenmu."

Wane 'yan siyasa gwamnan yake zargin da hannunsu?

Gwamnan ya ƙara da cewa alamu sun nuna akwai wasu 'yan siyasa da ke da hannu a duk irin waɗan nan kashe-kashen rayukan da ke faruwa a jihar ta Arewa maso Tsakiya.

“Abin takaici akwai alamun da ke nuna ayar tambaya kan wasu ‘yan siyasa a Filato game da wasu daga cikin wadannan tashe-tashen hankula saboda suna da alaƙa da masu haddasa rashin zaman lafiyan."

Kara karanta wannan

Direban Babbar Mota Ya Murkushe Jami'in Hukumar FRSC Har Lahira, Bidiyo Ya Bayyana

"'Yan siyasan suna da kashin kaji a jikinsu da ya kamata su amsa tambayoyi saboda suna da alaƙa ta kusa da wasu daga cikin masu haddasa wadannan tashe-tashen hankula."
“Na tabbata hukumomin tsaro suna kallon wannan karara. Waɗannan mutane ne waɗanda wasu lokuta suke amfani da addini da kabilanci don cimma burinsu na siyasa."

Dakarun Sojin Najeriya Sun Gano Masana'antar Kera Makamai a Jihar Kaduna

A wani rahoton kuma Dakarun sojin Najeriya sun gano wata masana'antar ƙera bindigu a ƙaramar hukumar Jema'a da ke kudancin Kaduna.

Sojojin sun kama wani hatsabibin mai sayar da makamai da suka jima suna nema ruwa a jallo, sun kama wani a masana'antar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel