Gwamnatin Najeriya
Bola Tinubu ya dauki alkawari talaka zai more idan ya kara hakuri. Shugaban kasa ya gana da wasu Sarakuna a fadar Aso Rock Villa, yace masu dadin yana gaba.
Gwamnatin Neja hada da gwamnatin tarayya, kamfanin wuta, kamfanonin Kainji Hydro Electric PLC da Mainstream Energy Solutions Limited ta maka a kotu.
Buba Galadima ya ce sun fadawa talakawa manufofin Tinubu a 2023 amma suka yi kunnen-kashi, yanzu ga shi za a dauke wasu ofisoshin CBN da hedikwatar FAAN zuwa Legas.
Majalisar kolin shari’a da addinin musulunci ta ce talakawa sun karu, mafi yawan jama’a suna neman abin da za su ci da Bola Tinubu ya karbi ragamar mulki.
A ranar Alhamis gwamnati ta ce ta dage ofishin hukumar filayen jiragen sama ta kasa (FAAN) daga Abuja zuwa Legas. Legit ta zakulo dalilai 7 na daukar wannan matakin.
Tafiye-tafiyen Bola Tinubu sun ci Naira biliyan 3.5 a yanzu. Tinubu ya ziyarci kasashe masu yawa saboda manufar inganta alaka, bunkasa tattalin arziki da zumunci.
Ministan Tsaron Najeriya, Badaru Abubakar ya gargadi 'yan Najeriya kan biyan kudaden fansa ga 'yan bindiga inda ya ce hakan kara lamarin zai yi a kasar.
Shugaban kwamitin da aka kafa domin gyara harkar haraji ya ce sun dauke kimanin N8tr daga cikin aljihun wasu mutane, sun shiga baitul-mali daga cire tallafin fetur.
A ranar Talata, 9 ga watan Junairu 2023, Bola Tinubu ya sanar da cewa ya zaftare adadin ayarin da ke yi masa rakiya, kafin ayi mako guda, har an saba alkawarin.
Gwamnatin Najeriya
Samu kari