Gwamnatin APC Ta Kai Karar Gwamnatin Tarayya Kotu a Kan Tsohon Bashin N138bn

Gwamnatin APC Ta Kai Karar Gwamnatin Tarayya Kotu a Kan Tsohon Bashin N138bn

  • Gwamnatin Neja ta kai karar ma’aikatar gwamnatin tarayya saboda zargin kin biyanta wasu hakkokinta
  • Hukumar kula da haraji ta jihar Neja tace rabon da ta karbi wadannan makudan kudi tun shekarar 2017
  • Idan an gama shari’a a kotun tarayyan da ke garin Minna, ana sa ran fiye da N100bn su shigo baitul-mali

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Niger - Hukumar da ke kula da harkar haraji a jihar Neja ta shigar da karar ma’aikatar makamashi ta tarayya a babban kotun tarayya.

Daily Trust tace an shigar da karar ne a kotun tarayya da ke zama a garin Minna, bisa zargin kin biyan kudin harajin da sun kai N138.1bn.

Gwamna
Gwamnatin jihar Neja Hoto: @HonBago
Asali: Twitter

Hukumar da ke da alhakin tattara harajin gwamnatin Neja ta gabatar da kararraki biyu a kotun na II, tana neman a biya ta hakkokin na ta.

Kara karanta wannan

EFCC za ta gurfanar da tsohon gwamna kan wani laifin da ya aikata lokacin yana ofis

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Neja tayi karar kamfanonin wuta

Wadanda ake kara sun kunshi kamfanin kula da harkar bashin lantarki da kamfanin Kainji Hydro Electric da Mainstream Energy Solutions.

Lauyan da ya tsayawa gwamnatin jihar a shari’ar mai lamba FHC/MN/CS/02/24 ya ce ana bin wadanda ake kara bashin haraji tun a 2017.

A doka akwai kudin kasa da gwamnati ta ke karba, an shaidawa kotu an yi shekara da shekaru ba a biya jihar Neja wadannan biliyoyi ba.

Ana so a biya jihar Neja N138bn

Aliyu Ibrahim Lemu, SAN ya bukaci a tursasawa gwamnati da kamfanonin da ake kara biyan bashin N116,133,882,800 na kudin kasa.

Rahoton yace shari’a mai lamba FHC/MN/CS/1/24 da Mohammed Ndayako, SAN ya shigar ya ce Neja tana ikirarin bin bashin N21.97bn.

An fara zama a kotu

Da aka zauna a kotun dazu, daya daga cikin lauyoyin Mohammed Ndayako, SAN, ya fadawa alkali cewa wadanda ake kara ba su zo ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Plateau ta sanya dokar hana fita na tsawon awanni 24, bayanai sun fito

Ganin ba za a iya yin shari’a da bangare daya ba, Abdullahi Muhammad Dan-Ige ya daga karar zuwa watan gobe domin jin ta bakin kowa.

Mai shari’a Abdullahi Dan-Ige ya ce za a sake zama a ranar 19 ga Fabrairu, zuwa lokacin ana sa ran an sanar da dukkanin lauyoyin.

Buba Galadima da gwamnatin APC

A cewar Buba Galadima, an fadawa talakawa manufofin Bola Tinubu amma suka yi kunnen-kashi wajen zabensa lokacin da aka yi takara.

Jagoran na jam’iyyar NNPP yace tun kafin zabe ya haskawa jama’a gwamnatin APC za ta karawa Legas karfi don haka bai tausayawa talaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel