Yadda Gwamna Ya Bar Aikin Gabansa, Ya Shilla Kasar Waje Aka Cashe na Kwanaki

Yadda Gwamna Ya Bar Aikin Gabansa, Ya Shilla Kasar Waje Aka Cashe na Kwanaki

  • An yi kwana da kwanaki Mai girma Babajide Sanwo-Olu bai Legas, ya tafi biki a wara kasar ketare
  • Ana zargin gwamnan jihar Legas yana cikin wadanda suka halarci bikin Aisha Achimugu @ 50
  • Miliyoyi sun yi ciwo a wannan biki da aka yi a tsibirin Grenada domin taya ‘yar kasuwar murna

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Lagos - A ranar Laraba ake zargin Mai girma Babajide Sanwo-Olu ya dawo Najeriya daga tsibirin Grenada inda ya halarci biki.

A wani rahoto da Premium Times ta kadaita da shi, an ce gwamnan na jihar Legas ya halarci bikin da Aisha Achimugu ta shirya.

Gwamnan Legas
Gwamnan Legas ya je Grenada Hoto: @jidesanwoolu
Asali: Twitter

Aisha Achimugu tayi biki a kasar ketaren inda manyan mutane suka cashe domin taya ‘yar kasuwar murnar cika shekaru 50.

Kara karanta wannan

EFCC za ta gurfanar da tsohon gwamna kan wani laifin da ya aikata lokacin yana ofis

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Sanwo Olu ya kashe $130, 000 a otel

Babajide Sanwo-Olu wanda ya zarce a 2023 ya dauki hayar jirgin yawo daga Najeriya zuwa tsibirin, kuma ya zauna a katafaren otel.

Rahoton yace otel din da gwamnan ya tare yana cikin mafi tsada a duniya, daga baya ya nuna aiki ya kai shi waje ba shakatawa ba.

Bincike ya sa an gano cewa a dakin da gwamna Sanwo Olu ya rika kwana a tsibirin Calivigny, ana biyan $132,000 a kowane dare.

Sanwo-Olu da sauran wadanda suka je wannan biki sun rika kwana ne a Calivigny Island da wani otel mai suna Silversand Grenada.

A tsawon kwanaki bakwai, ana tunanin an yi bindiga da $924,000 a kan wurin kwana ban da sauran kashe-kashen kudi da aka yi.

Gwamna ya je bikin Aisha Achimugu @50

Kara karanta wannan

Zargin cin hanci: EFCC za ta binciki ‘dan siyasar da ya fi kowa dadewa a majalisa

An fara gagarumin bikin da Aisha Achimugu ta shirya ne da liyafar kumallo a ranar 17 ga Junairu, haka aka yi gwangwaje har dare.

Jaridar tace Sanwo Olu bai iya zuwa ba sai bayan kwanaki biyu, a nan ya zauna har zuwa Talata, haka ya bar ofishinsa a Ikeja wayam.

Ina Gwamnan Legas ya shiga?

Jami’an gwamnatin jihar Legas sun yi kwana da kwanaki ba su san inda Babajide Sanwo-Olu ya shiga ba, an boye masu lamarin.

An sanar da wasu cewa aikin ofis ya kai gwamnan birnin Landan, wasu jami’an kuma sun tafi a kan ya tafi wasu harkoki ne a waje.

Hotunan da gwamnan ya fitar a X sun nuna ya hadu da Firayim Ministan Grenada, Dickon Mitchell, domin a kawowa Legas cigaba.

Ba a tabbatar da alakar gwamna da Achimugu ba, ko ya abin yake dai an shakata da wasannin Waje, Flavour, Adekunle Gold da Asake.

Asali: Legit.ng

Online view pixel