Atiku Ya Yi Sabon Bidiyo Ya Kira Tinubu da 'Bola' duk da APC Ta Yi Gargadi

Atiku Ya Yi Sabon Bidiyo Ya Kira Tinubu da 'Bola' duk da APC Ta Yi Gargadi

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya kira Shugaba Bola Tinubu da 'Bola' duk da gargaɗin da aka yi masa kan kiran shugaban da sunan
  • Atiku ya buƙaci ’yan Najeriya su karɓi katin zaɓensu, tare da yin amfani da shi wajen kada ƙuri’a domin kawar da jam’iyyar APC daga mulki a zaɓen 2027
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce zai yi aiki domin rage tsadar rayuwa da dawo da tsaro idan aka ba shi damar jagorantar Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su karɓi katin zaɓensu na PVC domin su kaɗa ƙuri’a a zaɓen 2027.

Atiku ya bayyana cewa zai yi aiki domin sauƙaƙa rayuwa da dawo da tsaron da ’yan Najeriya ke buƙata, yayin da ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da jefa jama’a cikin tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

INEC ta fadi dalilin cire sunan Pantami da sauran 'yan takara, ta ba su zabi

Atiku Abubakar da Bola Tinubu
Atiku Abubakar a hagu da Bola Tinubu a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Atiku Abubakar
Source: Facebook

A cikin saƙon da ya fitar a Facebook, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kira shugaban da sunan “Bola”, duk da sukar da ya fuskanta a baya kan kiran Tinubu da sunan.

Atiku ya buƙaci a karɓi PVC

Atiku ya bayyana cewa ya fahimci irin wahalhalun da ake fuskanta a faɗin Najeriya, inda ya lissafa matsalar abinci, tsadar sufuri da haya, da kuma matsalar tsaro.

Ya ce iyaye na kwanciya barci cikin damuwa kan yadda za su ciyar da ’ya’yansu washegari, yayin da wasu ’yan fansho ke shiga mawuyacin hali wajen zaɓar tsakanin sayen magani da abinci.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma ce matasa na aiki tuƙuru, amma kuɗin da suke samu ba sa wadatar musu saboda tsadar sufuri, haya da sauran buƙatun yau da kullum.

Ya ƙara da cewa iyalai da dama na rayuwa cikin fargabar sace mutane da hare-hare, tare da damuwa kan ko ’yan uwansu za su dawo gida lafiya.

Kara karanta wannan

Tinubu na tsaka mai wuya, jigon APC ta aika wasika ga shugaban Amurka kan zaben 2027

Atiku ya ce:

“Babu wani da ya kamata ya fuskanci yunwa da rashin tsaro a lokaci guda. Ba za mu bari wannan wahala da fargaba su zama makomar da ’ya’yanmu za su gada ba.
“Idan kana da rajistar zaɓe, don Allah ka je ka karɓi katin zaɓenka na PVC. Ka riƙe shi, domin shi ne muryarka, zaɓinka da ƙarfin da za ka yi amfani da shi cikin lumana wajen neman sauyi.”

Atiku zai rage tsadar rayuwa

Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da tsawwala rayuwa ga ’yan Najeriya, yana mai alƙawarin yin aiki domin rage tsadar kayayyaki da sauran buƙatun jama’a.

Ya ce zai mayar da hankali wajen samar da yanayin da iyalai za su iya rayuwa cikin mutunci, tsaro da fata na samun kyakkyawar makoma.

Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi
Atiku Abubakar da abokin takarar shi, Rotimi Amaechi. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

A saƙon nasa, ya yi kira ga matasa da manya da su haɗa kai domin zaɓar shugabancin da zai magance matsalolin da suke addabar ƙasar.

Kara karanta wannan

Shettima ya magantu a kan tsoron da 'yan Arewa ke ji a tazarcen Tinubu

Atiku ya ce:

“Bola ya tsawwala rayuwa. Zan yi aiki domin sake sauƙaƙa rayuwa da dawo da tsaron da kowane ɗan Najeriya ya cancanci samu.”

Ga bidiyon bayanin da Atiku ya yi a kasa:

Atiku ya gargadi INEC kan magudi

A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan naɗin wasu mutane biyu Yarbawa a muhimman sassan hukumar INEC.

Atiku ya bayyana matsayinsa ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Lahadi, inda ya nemi a yi bayani kan naɗin Oluyemi Titilayo Adeyemi-Showunmi da Dokta Lawrence Bayode.

An naɗa Adeyemi-Showunmi a matsayin shugabar sashen ayyukan zaɓe da rajistar masu zaɓe, yayin da Bayode ke jagorantar sashen fasahar sadarwa na zamani (ICT).

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng