Talaka Ya Tsokano Wuyan da Ake Ciki, Mun Gargade Shi Kafin Zabe Inji Tsohon Jigon APC

Talaka Ya Tsokano Wuyan da Ake Ciki, Mun Gargade Shi Kafin Zabe Inji Tsohon Jigon APC

  • Buba Galadima ya ce sun yi hasashen abubuwan da Bola Tinubu yake yi yau, sai aka ki sauraronsu
  • A lokacin zaben 2023, ‘dan siyasar ya nunawa jama’a cewa Rabiu Kwankwaso da NNPP ne mafita
  • Legit ta samu damar zantawa da Galadima wanda ya fada mata ra'ayinsa a kan gwamnatin APC

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja – Buba Galadima kwararren ‘dan siyasa ne wanda an dama da shi wajen neman yakin zabe a jam’iyyun APC, PDP da NNPP.

A wata hira ta musamman da Legit Hausa tayi da Injiniya Buba Galadima, ya nanata cewa ya yi hasashen yanayin da ake ciki a yanzu.

Buba Galadima
Buba Galadima ya yi magana kan gwamnatin APC Hoto: Getty, dailypost.ng
Asali: Getty Images

Buba Galadima ya yi gaskiya?

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Tinubu ya dage zai daurawa jam'iyyar APC da NNPP auren dole a Kano

Al’umma da kungiyoyin addini suna kukan kuncin rayuwa, ‘dan siyasar yace a lokacin zaben 2023 sai da suka ja-kunnen mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buba Galadima wanda yace bai son yi magana, ya nuna ya ankarar da jama’a cewa Bola Tinubu zai maida hankali ga Legas a mulkinsa.

Buba Galadima ya zargi talaka da taurin kai

"A wannan tafiyar da aka yi, duka bin da ka sani yana faruwa a wannan gwamnati, babu abin da ba mu fada ba kafin zabe."
"Mun ce za a koma Legas, mun ce za gyara barikin Dodan da sauransu, idan aka bibiya duk wadannan na zayyana su a kasa."
"Duk abubuwan da na fada ga shi ina ganinsu. Amma ni ina son talakan Arewa ya sha wuya."
"Ka na iya rubutawa domin kunnen kashi ne da shi. Abin da ba ka sani, idan ka samu wanda ya sani, sai ka yarda mana."

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya yi maganar ficewar Kwankwaso daga NNPP zuwa APC da takarar 2027

- Buba Galadima

Menene abin da ya hana NNPP sukar Tinubu?

Injiniyan ya ce yanzu ana surutun ba su cewa uffan, alhali a lokacin da suka rika kira ga jama’a su zabi Rabiu Kwankwaso, ba su tanka su ba.

Rabiu Kwankwaso da ya yi takara a NNPP ya zo na hudu ne bayan APC, PDP da LP.

Za ayi fito na fito da gwamnatin Tinubu

Watanni kadan da hawa mulki sai ga shi ana labarin za a dauke wasu ofisoshin CBN da hedikwatar FAAN daga birnin Abuja zuwa Legas.

Kungiyar dattawa ta ACF da Sanatocin jihohin Arewa sun soki wannan lamari, sun shirya kalubalantar gwamnatin tarayya ko a kotu ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng