Dalilai 7 da Yasa Gwamnatin Tarayya Ta Mayar da Wasu Sassan Hukumar FAAN Legas

Dalilai 7 da Yasa Gwamnatin Tarayya Ta Mayar da Wasu Sassan Hukumar FAAN Legas

  • Festus Keyamo ya fadi dalilan da suka saka gwamnati ta dauke hedikwatar hukumar FAAN daga Abuja zuwa Legas
  • Ministan jiragen saman, a ranar Alhamis ya sanar da hukuncin dauke hedikwatar, inda ya jaddada cewa babu kabilanci ko bangaranci a ciki
  • Legit Hausa ta zakulo wasu dalilai 7 daga sanarwar ministan da suka saka aka dauke hedikwatar hukumar zuwa Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - A ranar Alhamis gwamnatin tarayya ta sanar dasu cewa ta dauke ofishin hukumar filayen jiragen sama ta kasa (FAAN) daga Abuja zuwa Legas.

Ministan sufurin jiragen sama da sararin samaniya, Festus Keyamo ya sanar da hukuncin dauke ofishin hukumar a ranar Alhamis a wata sanarwa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Yanzu: Masu garkuwa da mutane sun kai hari rukunin gidajen sojoji a Abuja, sun sace mutane

Dalilan gwamnati na mayar da hedikwatar Hukumar FAAN zuwa Legas
Gwamnati ta fadi dalilai 7 da suka sa ta mayar da hedikwatar Hukumar FAAN zuwa Legas. Hoto: @FAAN_Official
Asali: Twitter

Gwamnatin Buhari ce ta mayar da ofishin Abuja

A shekarar 1976 ne aka kafa hukumar FAAN, amma sake fasalin dokar sufurin jiragen sama a shekarar 1995 ya sa gwamnati ta hade ayyukan hukumar NAA zuwa hukumar FAAN.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar na kula da dukkanin filayen jiragen sama mallakin gwamnatin tarayya, kuma an yi mata hedkwatar farko a Legas. Sai dai a 2020, Shugaba Buhari ya mayar da ofishin Abuja.

Sanarwar Ministan ta ce dauke hedikwatar hukumar daga Abuja zuwa Legas shi ne mafi alkairi ga Najeriya musamman ganin cewa ana hada-hadae kudaden jama'a a ciki.

Karanta sanarwar ministan a nan kasa:

Dalilai 7 na dage hedikwatar FAAN daga Abuja zuwa Legas

1. Rashin ofis ga ma'aikata

Ministan ya yi nuni da cewa babu wadatattun ofis ofis ga ma'aikata a hedikwatar da ke Abuja, hakan ya tilasta da yawan ma'aikata suka koma Legas.

Kara karanta wannan

Al Qalam: An samu karin bayani kan dalibai mata na jami'ar Katsina da aka sace

Ya ce tun farko an yi kuskuren maido da hedikwatar hukumar zuwa Abuja, la'akari da cewa babu wani gini guda daya mallakin FAAN wanda zai iya daukar dukkan ma'aikata.

2. Biyan ma'aikata alawus din DTA

Bayan da ma'aikatan suka koma Legas da aiki, hakan ya saka hukumar biyansu kudin alawus din DTA, saboda a hukumance kamar suna aiki ne a wajen ma'aikatar.

Ministan ya ce wannan barnatar da kudin jama'a ne kawai, don haka gwanda a mayar da hedikwatar Legas kowa ya huta.

3. Tsohon ginin hedikwatar na Legas zai lalace

Ministan sufurin jiragen saman ya kuma yi nuni da cewa ginin FAAN na Legas ya fara lalacewa saboda mutane ba sa zama a ciki.

Ya ce ana biyan miliyoyin kudi kowacce shekara don biyan kudin hayar ginin da hukumar ke aiki a ciki a Abuja, alhalin akwai na Legas.

4. Za a gina hedikwata a Abuja da Legas

Ministan ya bayyana cewa akwai shirin da gwamnati ta yi na gina ofishin hukumar a Legas da Abuja da zai wadatar da kowa.

Kara karanta wannan

FG ta saki sunayen kamfanonin Najeriya da suka cancanta su nemi kwangilar gwamnati a 2024

Amma ya ce har zuwa lokacin da za a kammala ginin, hukumar za ta ci gaba da amfani da ofishin ta na Legas wanda zai dauki daraktoci da manyan jami'ai.

5. Har yanzu ofishin hukumar na Abuja na aiki

Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa akwai ofisoshin hukumar da za su cigaba da aiki a Abuja ba tare da wani tsaiko ba.

Sai dai duk wani abu da ya shafi hedikwata zai koma Legas.

6. Abuja ko Legas, inda hedikwatar za ta zauna

Festus Keyamo ya ce nan gaba idan aka gama gina ofishin hukumar a Legas da Abuja, za a cimma matsaya kan garin da zai zama hedikwata.

7. Alkinta dukiyar jama'a

Keyamo ta ce ya yanke wannan hukunci ne don alkinta dukiyar jama'a ba wai bambancin kabila ko yanki ba ne kamar yadda wasu ke zargi.

Kotun Koli ta yanke hukunci kan zaben gwamnan Delta

Kara karanta wannan

Kano: Bayan nasara a kotu, Gwamnatin Kano ta magantu kan masu niyyar wawushe asusun jihar

A wani labarin, Kotun Koli a yau Juma'a 19 ga watan Janairu ta yanke hukuncin karshe kan karar da jam'iyyar APC da Omo-Agege suka shigar na neman a tsige Sheriff Omorevwori daga gwamnan Delta.

A hukuncin da kotun mai mambobi biyar ta yanke, Mai Shari'a John Okoro ya ce APC da dan takararta sun gaza gabatar da hujjoji da za su gamsar da kotun, don haka ta yi watsi da karar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel