Atiku Ya Jefawa Gwamnatin Tinubu Zafafan Tambayoyi 5 Kan Bashin $3.3bn da Aka Karbo

Atiku Ya Jefawa Gwamnatin Tinubu Zafafan Tambayoyi 5 Kan Bashin $3.3bn da Aka Karbo

  • Atiku Abubakar yace akwai ta-cewa game da bashin Dala biliyan 3.3 da aka karbo daga kasar waje
  • An ci bashin ne domin karfafa Naira a kasuwar canji, ‘dan takaran shugaban kasar ya nuna da walakin
  • Alhaji Atiku ya yi ikirarin sai Najeriya ta bada man $12bn kafin ta iya gama biyan bashin wannan daloli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Jagoran adawa kuma ‘dan takaran shugaban kasa a 2023, Atiku Abubakar, ya kalubalanci Bola Tinubu kan bashin NNPC na $3.3bn.

A wani dogon jawabi da ya yi a shafin X, Alhaji Atiku Abubakar yace akwai bukatar ayi bayanin dalolin da aka aro domin a karfafa Naira.

Atiku Abubakar da Bola Tinubu
Atiku da Shugaban kasa Hoto: Atiku Abubakar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A jawabin da ya fitar a ranar Alhamis, Atiku Abubakar yace bashin yana dauke da ruwan 12%, kuma za a biya ne danyen mai har na $12bn.

Kara karanta wannan

FAAN, CBN: Yadda muka yi da Sanata Ndume da ya kira ni a waya da dare - Okupe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wazirin Adamawa ya kuma jefawa gwamnatin tarayya kalubale kan dalilin amfani da SPV a kasar Bahamas da yace tana da kashi a gindinta.

$3.3bn: Atiku ya nemi Shugaba Tinubu ya yi magana

‘Dan takaran na 2023 yace abin mamakin shi ne har yanzu gwamnatin tarayya tayi gum game da lamari, tun Agustan bara babu wani bayani.

"Idan jama’a sun samu bayani a kan bashin shi ne gajeren jawabin da NNPCL ya fitar."
"Abin da ya fi rikitarwa a yarjejeniyar nan shi ne me zai jawo gwamnatin tarayya tayi rajistar kamfani a Bahamas alhali ta san badakalar kasar?"

- Atiku Abubakar

Atiku ya ce za a bada man $12bn a kan bashin $3bn

A cewar Atiku, ana hako ganguna miliyan 1.38 ne duk rana a 2024, sai ga shi za ta rika cire ganguna 90, 000 duk rana domin a biya bashin.

Kara karanta wannan

Yanzu Nan: Kwanaki 3 da Suka Wuce Tinubu Ya Saki Kudin Manyan Ayyuka 3 Inji Minista

Lissafin Atiku ya nuna za a bada ganguna miliyan 164.25 wanda darajarsu ya kai $12bn a farashin kasuwar yau domin biyan bashin $3.3bn.

Tambayoyin Atiku Abubakar?

1. Gwamnatin tarayya ta karbo bashin nan?

2. Bashin ya shiga cikin tsarin kudin da aka amince a majalisar tarayya gwamnati ta karbo aro?

3. Su wanene da hannu wajen bashin, kuma wace rawa za su taka wajen biya?

4. Su menene sharudan bashin da kuma mai bada bashin, ka’idar biyan kudin, jingina da kuma ruwa?

5. A karshe, menene dalilin rajistar SPV a Bahama alhali an san danyen badakalar kasar da tashen da tayi wajen boye kazaman dukiyoyi?

Karanci da tsadar Dala a Najeriya

Kuna da labari ‘yan kasuwan da ke shigo da kaya daga kasashen waje ba su samun Dala cikin sauki ko da araha, shiyasa ake fito da dabaru.

Wata jarida ta fara bankado yadda za ayi amfani da arzikin Najeriya wajen biyan bashin Afrexim da aka ci da nufin sauko da farashin Dala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel