Magana Ta Bambanta: APC Ta Faɗi Gaskiya kan Rigimar Wike da Gwamnoninta
- Jam’iyyar APC ta musanta rahotannin rikici tsakanin gwamnoninta da Nyesom Wike, tana mai cewa babu wata takaddama tsakaninsu kan zaɓen 2027
- Felix Morka ya ce gwamnonin APC da Wike sun haɗu wajen tallafa wa Shugaba Bola Tinubu domin sake zaɓensa a babban zaɓen 2027
- Kakakin APC ya bayyana shigar ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu a matsayin sabon mataki a dimokuraɗiyyar Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kakakin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Felix Morka, ya yi magana kan rigima da Nyesom Wike.
Morka ya yi watsi da rahotannin da ke cewa akwai saɓani tsakanin gwamnonin jam’iyyar da ministan Abuja, Nyesom Wike.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV a shirin News Day, bayan shigar Wike cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC.
APC ta musanta rigima da Wike
Morka ya ce zargin saɓanin da ake yi tsakanin ɓangarorin biyu ba gaskiya ba ne, domin dukkansu suna da ƙwarin gwiwar tallafa wa Shugaba Bola Tinubu domin sake zaɓensa a babban zaɓen 2027.
Ya ce:
“Tun farko, wannan rikici ƙarya ne. A ganina, babu wani rikici na gaske tsakanin waɗannan ɓangarori, domin sun haɗu wajen nuna ƙwarin gwiwarsu na musamman ga sake zaɓen shugaban ƙasa."
Ya bayyana cewa ƙungiyar gwamnonin APC ta ƙunshi gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin inuwar jam’iyyar, yayin da Wike, tsohon gwamnan Rivers, yake cikin majalisar ministocin Tinubu kuma yana goyon bayansa sosai.
A cewarsa, muradunsu na siyasa iri ɗaya ne, saboda haka rahotannin da ke nuna cewa akwai saɓani tsakaninsu ba su da wani muhimmanci sosai.

Source: Facebook
APC ta magantu kan kwamitin kamfen Tinubu
Morka ya ce fitar da jerin sunayen mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ya kuma fayyace matsayin mutanen da za su taka rawa wajen kamfen ɗin Tinubu.
Ya yi nuni da shigar gwamnonin da ba ‘yan APC ba cikin kwamitin, yana mai cewa hakan ya nuna yadda Tinubu ke iya samun goyon baya daga ɓangarorin siyasa daban-daban.
“Gwamnonin da ba ‘yan APC ba ne yanzu suna kan gaba wajen tsara wasu daga cikin ayyukanmu a yankunansu."
- in ji shi.
Kakakin APC ya bayyana wannan ci gaba a matsayin sabon mataki a siyasar dimokuraɗiyyar Najeriya, yana mai cewa shugaban ƙasar yana haɗa ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban domin cimma manufa guda.
Ya bayyana cewa haɗin gwiwar ba kasafai ake ganin irinsa ba a tsarin shugaban ƙasa, inda ake sa ran jam’iyyun siyasa za su fafata da juna.
A cewar Morka, Tinubu yana ƙetare bambance-bambancen jam’iyyu ta hanyar gina haɗin gwiwar ‘yan siyasa domin tallafa wa gwamnatinsa da yaƙin neman zaɓensa.
Ya ce:
“Muna ganin shugaban ƙasa da ke ƙetare dukkan bambance-bambance, yana kawar da abin da nake kira siyasar rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yan jam’iyyu, tare da haɗa su ƙarƙashin inuwa guda domin cimma manufa ɗaya don amfanin al’umma."
Wike ya naɗa kansa daraktan kamfen Tinubu
A wani labarin, an ji cewa Nyesom Wike ya ayyana kansa a matsayin jagoran yakin neman sake zaben Bola Tinubu a Abuja a 2027.
Ya hada kan wasu mambobin APC da PDP da zau su taimaka wajen tabbatar da nasarar shugaban kasa.
Wike ya kare manufofin tattalin arzikin Tinubu, yana mai cewa sauye-sauyen sun kawo wa Abuja cigaba.
Asali: Legit.ng


