FAAN, CBN: Yadda Muka Yi da Sanata Ndume da Ya Kira Ni a Waya da Dare, Okupe

FAAN, CBN: Yadda Muka Yi da Sanata Ndume da Ya Kira Ni a Waya da Dare, Okupe

  • Doyin Okupe ya bada labarin wayarsa da Muhammad Ali Ndume a kan shirin dauke ofisoshi zuwa Legas
  • Sanatan jihar Borno ta Kudu a majalisa bai goyon bayan janye ofioshin CBN da FAAN daga garin Abuja
  • Bayan ya soki Sanata Ali Ndume, Dr. Okupe ya fahimci abin da ‘dan majalisar yake kokarin haskawa yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Doyin Okupe wanda ya rike Darekta Janar na kwamitin yakin zaben Peter Obi ya yi magana game da surutun da ake tayi a ko ina.

Shirin maida wasu ofisoshin CBN da hedikwatar hukumar FAAN garin Legas ya jawo abin magana, musamman a yankin Arewacin kasa.

Bankin CBN
FAAN da wasu ofisoshin CBN za su koma Legas Hoto: www.centralbanking.com
Asali: UGC

Doyin Okupe ya yi Allah-wadai da jin wasu kalamai da suka fito daga bakin Muhammad Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu.

Kara karanta wannan

Atiku ya jefawa Gwamnatin Tinubu zafafan tambayoyi 5 kan bashin $3.3bn da aka ci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Muhammad Ali Ndume yana da ra’ayin cewa matakin da gwamnatin Bola Tinubu ta dauka yana da mummunan tasiri a siyasa.

Wasikar Doyin Okupe a kan Ali Ndume

A matsayinsa na ‘dan majalisa kuma jagora a jam’iyyar APC da ke mulki, Dr. Okupe yana ganin maganganun ba su dace da Ndume ba.

Da yake magana a dandalin X a tsakiyar makon nan, tsohon hadimin na shugabannin Najeriya ya yi tir da kalaman Sanatan.

Ba a dade ba kuma sai aka ji Okupe yana yabawa Sanata Ndume duk da sabaninsu.

Yadda batun ya faro

Da farko Okupe ya soki Ndume a kan matsayarsa, ya tuna masa cewa akwai bukatar a guji abin da zai jawo rashin zaman lafiya a kasa.

Kwararren likitan yana ganin siyasar Najeriya ba tayi kwarin da za a rika sakin baki ba, akasin ra'ayin kungiyar dattawan da ke Arewa.

Kara karanta wannan

Yanzu Nan: Kwanaki 3 da Suka Wuce Tinubu Ya Saki Kudin Manyan Ayyuka 3 Inji Minista

Can sai ga shi yana cewa Sanatan na kudancin Borno ya kira shi cikin dare a waya, kuma sun tattauna batun da kyau, an samu fahimta.

Maganar Okupe yana yabawa Sanata Ndume

“Sanata Ndume @Malindume ya kira ni kuma mun yi magana sosai na fiye da mintuna 30."
"Halayyarsa, gasiyarsa, da amannarsa ga jam’iyyarsa da shugaban kasa sun burge ni.
"Yana nufin alheri, amma shakka babu akwai cikas a fadar shugaban kasa da ba su taimaka wajen tattauna da kyau a kan tsare-tsare ba.
"Ina girmama shi yanzu."

- Muhammad Ali Ndume

Atiku ya soki bashin Tinubu

A watan nan aka karbi $2.25bn daga bashin $3.3bn daga Afrexim, an ji labari Atiku Abubakar yace za a biya bashin ne da danyen mai.

Baya ga tulin ruwa a cikin bashin, Wazirin Adamawa yace za a bada gangunan mai miliyan 164 wanda darajarsu a kasuwa ta kai $12bn.

Asali: Legit.ng

Online view pixel