Yanzu Nan: Kwanaki 3 da Suka Wuce Tinubu Ya Saki Kudin Manyan Ayyuka 3 Inji Minista

Yanzu Nan: Kwanaki 3 da Suka Wuce Tinubu Ya Saki Kudin Manyan Ayyuka 3 Inji Minista

  • Bola Ahmed Tinubu ya fitar da kudi domin a cigaba da aikin hanyar Abuja-Kaduna-Zariya-Kano
  • Ministan ayyuka watau David Umahi ya sanar da haka da ya je duba wani babban titi da ake yi
  • Gwamnatin tarayya ta dauko wadannan ayyuka tituna lokacin Muhammadu Buhari yana ofis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ministan ayyuka na kasa, David Umahi yace Bola Ahmed Tinubu ya amince da kudin wasu manyan kwangilolin hanyoyi.

The Nation ta rahoto Sanata David Umahi yana cewa Bola Ahmed Tinubu ya yarda da kudin da za a kashe a titin Legas-Ibadan.

Titi.
Wani titi a Najeriya Hoto: www.julius-berger.com
Asali: UGC

Mai girma shugaban kasan ya waiwayi batun gadoji biyu da za ayi a titin ‘Second Niger’ da ya hada Neja-Delta da Kudu maso gabas.

Kara karanta wannan

Talaka ya tsokano wuyan da ake ciki, mun gargade shi kafin zabe – Tsohon Jigon APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan yace an yi na’am da kudin da za a kashe domin karasa aikin titin Abuja-Kaduna-Zaria-Kano wanda gwamnati ta fara tun tuni.

Wannan mataki da shugaban kasa ya dauka yana nufin an cire kalubalen da ake fuskanta ta bangaren tattalin arziki wajen ayyukan.

Ministan ya yi wannan jawabi a lokacin da ya duba aikin da ake yi a babbar hanyar Lafiya da na fadada titin Enugu- Otukpo-Makurdi.

Gwamnan jihar Benuwai, Rabaren Hyacinth Alia yana wajen da ministan ya yi magana.

Kamfanin China Harbour Nigeria Limited, gwamnatin tarayya da wani banki za su hada-kai wajen aikin hanyar da ta ratsa jihohi uku.

Daily Nigerian tace Sanata Umahi ya shaida cewa ana sa ran kammala titin a watanni 48.

Ministan ya yi amfani da daman ya godewa Tinubu, yace kwanaki uku da suka wuce ya yi umarnin karasa aikin Abuja-Kaduna-Kano.

Kara karanta wannan

Zargin cin hanci: EFCC za ta binciki ‘dan siyasar da ya fi kowa dadewa a majalisa

Kudin titin Abuja-Kaduna-Zariya-Kano ya fito

"Labarin farin ciki ne a wuri na, mun samu cikas a kudin aikin amma Mai girma Shugaban kasa ya magance matsalar"
"(Tinubu) ya umarci a saki kudi da gaggawa domin cigaba da aikin hanyar nan. Haka titin Legas-Ibadan da gadojin titin Neja."

- David Umahi

Asali: Legit.ng

Online view pixel