Magana Ta Girma: IMF Ta Tsoma Baki kan Maganar Dawo da Tallafi a Najeriya

Magana Ta Girma: IMF Ta Tsoma Baki kan Maganar Dawo da Tallafi a Najeriya

  • Asusun ba da limuni ta duniya, MF ya yi magana game da maganganu kan dawo da tallafin mai a Najeriya a halin yanzu
  • IMF ta ce tallafin man fetur yana kashe kuɗaɗen gwamnati sosai, yana fifita masu kuɗi, tare da ƙara matsin tattalin arziki da hauhawar farashi
  • Asusun ya ba da shawarar tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi ta hanyar rage kuɗin sufuri, shirin ciyar da ɗalibai da taimakon manoma masu rauni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya shawarci Najeriya game da maganar dawo da tallafin mai.

IMF ya gargadi kasar da kada ta dawo da tallafin man fetur ga kowa, inda ya ba da shawarar tallafa wa iyalai masu ƙaramin ƙarfi domin rage musu radadin tsadar makamashi.

An gargadi Tinubu kan dawo da tallafin mai
Shugaba Bola Tinubu yayin taron majalisar zartarwa a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Rodrigo Valdés, daraktan sashen kula da harkokin kuɗaɗen gwamnati na IMF, ya yi wannan bayani yayin taron manema labarai, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Tsugune ba ta kare ba, Amurka ta sake barazanar janye taimakonta ga Najeriya

IMF ta ce tallafin man fetur ga kowa yana cin kuɗaɗen gwamnati masu yawa, yana kuma fi amfanar masu kuɗi, tare da ƙara matsin tattalin arziki a lokacin da kuɗin rance ke ƙaruwa.

An gudanar da taron ne a yayin taron shekara-shekara na IMF da Bankin Duniya na shekarar 2026, a Bangkok, Thailand, ranar Laraba.

Tambayar da aka yi wa Valdés ta shafi yadda asusun zai ba da shawarar barin farashin makamashi ya dace da ƙarancinsa, alhali tsadar man fetur a Najeriya na iya ƙara kuɗin sufuri, haifar da hauhawar farashi da zurfafa talauci.

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake matsa wa gwamnatin Najeriya lamba ta dawo da tallafin man fetur gabanin shekarar zaɓe.

Ya bayyana cewa tallafin man fetur ko matakan hana farashi sauyawa yadda ya kamata sakamakon tashin farashin makamashi sun jawo wa ƙasashe asarar kuɗi da ta kai tsakanin kashi ɗaya zuwa kashi 1.5 na jimillar kuɗaɗen da tattalin arzikinsu ke samarwa (GDP) a shekarar 2026.

Valdés ya ce:

“Kare mutane ba yana nufin kare farashin man fetur ba ne.”
“Na farko, yana kashe kuɗaɗen gwamnati masu yawa sosai. Na biyu kuma, idan aka duba yadda ake amfani da man fetur, za a fahimci cewa tallafin yana yawan fifita masu kuɗi a wurare da dama.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta kare farashin mai, ta magantu kan yiwuwar dawo da tallafi

Valdés ya shawarci gwamnatoci su mayar da hankali kan shirye-shiryen tallafa wa jama'a da kuma amfani da bayanan iyalai domin gano mutanen da suka fi buƙatar taimako.

Gwamnati ta ƙaddamar da rangwamen man fetur

Gwamnatin tarayya ta sanar da bayar da rangwamen man fetur na tsawon kwanaki 30 a gidajen sayar da man fetur na Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) Limited.

Gwamnatin ta ce za a ba masu zirga-zirgar jama'a fifiko a shirin domin rage musu nauyin tsadar man fetur.

Taiwo Oyedele, ministan kuɗi, ya ce gidajen sayar da man fetur na NNPC za su sayar da shi a farashin da suka saya, ta hanyar barin ribar da suke samu daga cinikin.

Ya bayyana cewa matakin na ɗan lokaci ne domin rage wa jama'a raɗaɗin tsadar man fetur, ba wai dawo da tallafin man fetur ba ne.

Gwamnatin ta kuma gabatar da shawarar tattaunawa domin sanya iyakar farashin man fetur da ake sayarwa daga matatar mai ko farashin saukar da shi a tashar jiragen ruwa a kan naira 1,350 kan kowace lita.

Kara karanta wannan

'Ku cire rai kan dawo da tallafin mai': Ƴar takarar shugaban ƙasa ta zare idanu

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.