Najeriya Ta Zo Ta 1 a Talauci a Duniya, Mutum Miliyan 17 Sun Talauce
- Najeriya ta shiga yanayi mafi girma a duniya na al'ummar da ke rayuwa a cikin talauci a fannoni daban-daban inda mutane miliyan 17.9 suka koma cikin talauci
- Rahoton 2026 da Majalisar Dinkin Duniya da cibiyar Oxford suka fitar ya nuna cewa Najeriya ta samu koma baya bayan samun ci gaba da aka yi tsakanin 2018 da 2021
- Yanzu haka adadin 'yan Najeriya da ke cikin matsin talauci ya kai miliyan 113.32, wanda hakan ke wakiltar kashi 48.7 na al'ummar kasar baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Sabon rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya na UNDP tare da Cibiyar Oxford ta Nazarin Talauci da Tattalin Arziki suka fitar ya nuna cewa Najeriya ce ke kan gaba a duniya wajen ƙaruwar adadin mutanen da suka fada cikin talauci
Rahoto ya nuna cewa karuwar 'yan Najeriya miliyan 17.9 a tsakanin shekarar 2021 zuwa 2024 ya wuce adadin kasar Afghanistan wadda ta samu karuwar mutane miliyan 5.3 a cikin irin wannan lokacin.

Source: Facebook
Miliyoyin 'yan Najeriya sun talauce
Punch ta wallafa cewa cikin bayanin rahoton, an nuna cewa tsarin auna talaucin ya wuce kan maganar kudin shiga kadai, inda ya haɗa da rashin damar samun ingantaccen ilimi.
Rahoton ya kara da cewa ya shafi kula da lafiya, wutar lantarki, ruwan sha mai kyau, muhalli mai tsafta, da abinci mai gina jiki.
Adadin 'yan Najeriya da talaucin ya shafa ya haura daga miliyan 72.21 a shekarar 2021 zuwa miliyan 90.07 a shekarar 2024 a ma'aunin binciken da aka yi aiki da shi.
Rahoyon the Cable ya nuna cewa ƙididdigar shekarar 2024 ta ƙasa ta nuna cewa 'yan Najeriya miliyan 113.32 ne ke cikin matsanancin talauci.
Jihohin Kebbi, Yobe, da Sokoto ne suka fi fuskantar wannan kalubale, yayin da jihar Lagos ke da mafi karancin adadi.
Kwararren farfesa a fannin tattalin arzikin siyasa, Pat Utomi, ya yi gargadin cewa karuwar talauci, yunwa, da rashin tsaro suna tura 'yan Najeriya zuwa ga matsanancin haɗari, yana mai buƙatar daukar matakan gaggawa gabanin zaɓukan 2027.

Source: Twitter
Halin da Ake Ciki a Matakin Duniya
A tsakankanin kasashen duniya, rahoton ya kimanta cewa mutane biliyan 1.2 ke rayuwa a cikin matsanancin talauci inda fiye da rabinsu, mutane miliyan 616, suke a yankin kudu da hamada a Africa.
Sama da yara miliyan 617 da shekarunsu ba su kai 18 ba ne ke fuskantar wannan matsin talauci a duniya, wanda ke nufin kusan ɗaya daga cikin yara uku na cikin matsanancin talauci idan aka kwatanta da babba ɗaya cikin mutane bakwai.
An rufe bankuna 476 a Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa Bankunan Kasuwanci da na Zuba Jari a Najeriya sun rufe rassan bankuna da cibiyoyin ma'amalar kuɗi guda 476 tsakanin shekarar 2022 zuwa 2025.
Alƙaluman Babban Bankin Najeriya (CBN) sun nuna cewa adadin rassan bankunan ya ragu daga 5,410 a shekarar 2022 zuwa 4,934 a shekarar 2025, wanda ke wakiltar raguwar kashi 8.8 a shekara uku.
Mafi yawan waɗannan rassa, wato kusan kashi 92% na rufe rassan, sun faru ne tsakanin shekarar 2024 da 2025 duk da cewa an samu karuwar adadin bankunan da ke gudanar da aiki a ƙasar.
Asali: Legit.ng

