Bola Tinubu Ya Hadu da Sarakuna, Yayi Masu Godiya Amma Ya Roki Taimako 1

Bola Tinubu Ya Hadu da Sarakuna, Yayi Masu Godiya Amma Ya Roki Taimako 1

  • Bola Ahmed Tinubu ya zauna da sarakunan yankin Kudu maso kudu a wata ziyara da suka kawo masa
  • Shugaban Najeriyan ya yi alkawarin magance matsalolin mutanen yankin Neja-Delta a gwamnatinsa
  • Mai girma Bola Tinubu ya nemi jama’a su kara yin hakuri da wahalar da manufofinsa suka jefa su

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya dauki alkawari cewa kwanan nan mutanen Najeriya za su ji dadin manufofin da ya kawo a mulkinsa.

Shugaban kasar ya ce wadannan tsare-tsare da aka fito da su masu tsauri sun zama dole domin Najeriya ta cigaba a cewar Daily Trust.

Tinubu
Bola Tinubu da Sarakunan Neja-Delta Hoto: @Dolusegun16
Asali: Twitter

Haduwar Bola Tinubu da Sarakuna

Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya sha wannan alwashi ne a lokacin da ya yi zama da sarakunan yankin Kudu maso kudu a Abuja.

Kara karanta wannan

"An yi masa mugun duka": Shehu Sani ya yi martani yayin da shugaban makarantar Kaduna ya shaki yanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar sarakunan kudancin kasar a karkashin jagorancin Mai martaba Janar Felix Mujakperuo mai ritaya sun je fadar Aso Villa.

Manjo Janar Felix Mujakperuo ya yi jawabi a madadin sauran takwarorinsa a ranar Talata, ya yi kira ga shugaban kasa ya duba kokensu.

Shugaban kasa Tinubu yayi godiya

Bola Tinubu ya yabawa sarakunan a kan yadda suka fahimce shi tare da goyon bayan shi musamman bayan ya cire tallafin man fetur.

An rahoto cewa shugaban kasar ya yi wa sarakunan alkawari cewa gwamnatinsa za ta magance matsalolin da suka shafi yankin na su.

...Tinubu ya roki a sa shi a addu'a

Tinubu ya shaidawa masu martaban irin kokarin da yake yi na kawo karshen matsalolin sauyin yanayi da abubuwan more rayuwa.

Gwamnatin Tinubu za ta tsabtace yanayin Neja-Delta tare da kawo cigaban al’umma, amma yana bukatar sarakunan su sa shi a addu'o'insu.

Kara karanta wannan

"Kada ku mayar da kudi Ubangijinku": Tinubu ya ba shugabannin Kirista babban aiki 1 tak

An yi shekara da shekaru ana barna, shugaban kasar yace zai farfado da tattalin arziki, amma dole yana bukatara addu’ar manyan.

Ajuri Ngelale ya fitar da jawabi inda ya nuna shugaban kasar yace zai sharewa Neja-Delta duk kukanta kuma ana hango alamun nasara.

Buba Galadima ya soki tikitin Tinubu

Ana da labarin yadda jam’iyyar APC da Bola Tinubu tayi amfani da musulunci wajen samun kuri’un musulmai a babban zabe da aka yi a 2023.

Injiniya Buba Galadima yace babu wanda ya san halin ‘dan siyasa da kyau kamar abokinsa don haka bai kamata talaka ya bari a rude shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel