NSCIA: Malaman Musulunci Sun Koka Kan Halin da Gwamnatin Tinubu Ta Jefa Al’umma

NSCIA: Malaman Musulunci Sun Koka Kan Halin da Gwamnatin Tinubu Ta Jefa Al’umma

  • Majalisar NSCIA ta addinin musulunci ta ce mutane suna wahala saboda tsadar da man fetur ya yi
  • Farfesa Is-haq Akintola ya ce talakawa sun karu, mafi yawan jama’a suna neman abin da za su ci
  • Gwamnati ta kawo mawuyatan tsare-tsare da Bola Tinubu ya karbi ragamar mulki a Mayun 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Majalisar kolin shari’a da addinin musulunci watau NSCIA ta nuna takaicinta a kan halin da ake ciki bayan cire tallafin fetur.

Vanguard ta ce sakataren NSCIA na kasa, Farfesa Is-haq Akintola a wani jawabi da a fitar, ya ce sun damu da yanayin al’umma a yau.

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya cire tallafin fetur Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jawabin Farfesa Is-haq Akintola ya nuna mutane suna cikin mawuyacin halin tattalin arziki a sakamakon janye tallafi na fetur.

Kara karanta wannan

"A nemo mun ita: Bidiyon wata yar makaranta tana Sallah a kan hanya ya dauka hankalin jama'a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Majalisar (NSCIA) tana sane da cewa kalubalen da ake ciki sun yi yawa domin wadanda ke farfadowa daga fargabar ta’addanci da rashin tsaro sun ci karo da matsalolin tattalin arziki da har lamarin ya kai bukatun yau da gobe sun yi wa mafi yawan Musulmai wahala.
"A mafi yawan gidaje, ana neman yadda za a rayuwa ne yayin da adadin marasa hali yake cigaba da karuwa a cikin al’umma."

- Farfesa Is-haq Akintola

Wani kokari ake yi wa musulmai?

Domin ganin an taimakawa marasa karfi, Is-haq Akintola yace suka fito da tsarin MESH wanda yake tallafawa jama’a tun a 2016.

MESH ya taimakawa jama’a a bangaren ilmi, kiwon lafiya da walwala kuma har gobe a ba a gajiya ba ganin halin da jama’a ke ciki.

NSCIA ta ce dole sai gwamnatocin tarayya da jihohi sun tashi tsaye wajen taimakawa marasa karfi bayan cire tallafin fetur.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya nuna gwamnan arewa 1, ya bayyana ayyukan Alherin da Yake Zuba Wa Talakawa

Ana ware Musulmai wajen bada taimako

Rahoton ya ce kukan da majalisar take yi shi ne akwai jihohin da ake maida musulmai saniyar ware wajen rage radadin rayuwa.

Akintola ya ce daga cikin jihohon da ake zargin an yi watsi da musulmai akwai jihar Filato.

Manyan Arewa sun koka da gwamnati

Ana da labari dattawan Arewa sun ce akwai take-taken nakasa mutanen yankinta a shirin gwamnatin tarayya na dauke FAAN da CBN.

ACF ta ce maida hedikwatoci Legas zai jawo Abuja ta zama kango kamar yadda Olusegun Obasanjo ya yi da ya karbi mulki a 1999.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel