Daga Yin Kwana 7 Har Tinubu Ya Shure Umarnin da Ya Bada Domin Rage Facakar Kudi

Daga Yin Kwana 7 Har Tinubu Ya Shure Umarnin da Ya Bada Domin Rage Facakar Kudi

  • Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa ya zaftare adadin ayarin da ke yi masa rakiya
  • Idan zai yi tafiya a gida ko waje, umarni ya zo cewa masu bin shugaban Najeriyan za su rage yawa
  • Shugaban kasar ya je jihar Imo a makon nan dauke da mutanen da sun zarce 25 da ya dauki alkawari

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada. s

Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sabawa sabon umarnin da ya bada na rage adadin masu bin sa wajen yin tafiye-tafiye.

Rahoton da aka samu daga Premium Times ya ce shugaban kasar ya yi watsi da umarnin da ya bada da kan shi a Junairun nan.

Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a Imo Hoto: @Hope_Uzodimma1
Asali: Twitter

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Ajuri Ngelale ya nuna an dauki matakin ne domin rage kashe kudin gwamnati.

Kara karanta wannan

Ayi Hakuri: Dalilin neman afuwar ‘Yan Najeriya kan wahalar da na Jefa su – Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu a jihar Imo

Kafin tafiya tayi nisa, sai ga shi shugaba Bola Tinubu ya ziyarci garin Owerri a jihar Imo da irin ayarin da aka saba ganin sa da shi.

Jaridar ta ce wadanda suka yi wa Tinubu rakiya zuwa wajen sake rantsar da gwamna Hope Uzodinma sun zarce mutum 50.

Umarnin da aka bada kuwa shi ne ayarin shugaban kasa ba zai wuce mutane 25 a gida da kuma mutane 20 a tafiyar ketare ba.

Mutane 25 jirgin shugaban kasa ya dauka zuwa Owerri, amma bayanai sun nuna akwai wasu 30 da aka tura Imo kafin lokacin.

Ayarin Tinubu a jirgin NAF 001

A jirgin NAF 001 an dauki Seyi Tinubu, Aderemi Damilotun, Hakeem Muri-Okunolam Subair Oluwatoyin da kuma Atika Ajaka.

Jirgin yana dauke da Kamorudeen Yusuf, Wale Fadare, Ajuri Ngelale, Victor Adeleke, Fasasi Adegboyega sai Nurudeen Yusuf.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi halin Buhari 1 da ya burge shi, ya ce ya shammace shi bayan barin mulki

Har ila yau jirgin fadar na NAF 001 ya dauki Usman Shugaba, Dr Tinubu Sikiru Adekunle, Bashir Mohammed da Musa Yakubu.

Sauran wadanda ke cikin tawagar su ne masu daukar hoto (Asemota Nosa Joseph and Okanlawon Taiwo) da ‘yan jaridan NTA biyu.

Baya ga Musbau Danwahab da Lukman Sani daga NTA, akwai Sunday Moses wanda yake yi wa shugaban Najeriya Bola Tinubu bidiyo.

Abdulaziz Abdulaziz da wasu jami’an yada labarai biyar da jami’an tsaro 15 da sojoji da ma’aikata kamar direbobi sun isa Owerri tuni.

Afuwar shugaba Muhammadu Buhari

A jiya aka ji labari tsohon shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana game da gwamnatin da ya jagoranta tun daga 2015 zuwa 2023.

Shugaba Buhari ya ce ganin wasu sun tagayyara a mulkinsa, shiyasa mutane hakuri a karshen wa’adinsu a ofis kafin karshen Mayun bara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel