Tsugune ba Ta Kare ba, Amurka Ta Sake Barazanar Janye Taimakonta ga Najeriya
- Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da amfani da yara a yaƙi, tare da barazanar dakatar da tallafin soji
- Rahoton Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya zargi Boko Haram da ISWAP da ɗaukar yara masu shekaru 12 domin ayyukan yaƙi
- Amurka ta ce Najeriya ta gaza cika ƙa’idojin yaƙi da fataucin mutane tsawon shekaru 15, yayin da tallafin da gwamnati ke bayar wa ya ragu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da suka saba ka'ida wurin amfani da yara a yaki.
Sabar dokar mai kare amfani da yara a yaki za ta jawo Amurka ta haramta wa Najeriya ba ta tallafin soji, saboda zargin amfani da yara a rikice-rikice.

Source: Getty Images
Rahoton, wanda aka wallafa ranar 11 ga Oktoba, kuma jaridar Punch ta samu ranar Litinin, ya shafi lokacin daga 1 ga Afrilu, 2025 zuwa 31 ga Maris, 2026.
Musabbabin shirin kakaba takunkumi ga Najeriya
Matakin na iya janyo dakatar da horar da sojoji, sayar da makamai, tallafin kuɗaɗen soji da haɗin gwiwar tsaro daga ranar 1 ga Oktoba, 2026, sai dai idan Shugaba Donald Trump ya bayar da rangwame.
Wannan mataki ya biyo bayan rahoton Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka na shekarar 2026 kan fataucin mutane, wanda ya nuna cewa Boko Haram da ƙungiyar ISWAP na ci gaba da ɗaukar yara da amfani da su a Najeriya.
Wannan shi ne sabon rahoton da ake da shi kan yadda Najeriya ke yaƙi da fataucin mutane.
Rahoton ya sanya Najeriya cikin ƙasashe 14 da ake zargi da ɗaukar yara ko amfani da su a yaƙi, ciki har da Rasha, Iran, Sudan ta Kudu da Somaliya.
Majiyoyi suka ce rahoton ya kuma bayyana cewa Najeriya ta gaza cika mafi ƙarancin ƙa’idojin yaƙi da fataucin mutane a karo na 15 a jere.
A cewar rahoton, gwamnatocin da aka sanya cikin jerin za su fuskanci takunkumi a shekara ta kuɗi mai zuwa kan wasu tallafin tsaro da lasisin kasuwanci na kayan aikin soji.
Dokar CSPA ta haramta bai wa gwamnatocin da ke cikin jerin wasu tallafi, ciki har da horar da sojoji, tallafin kuɗaɗen soji, kayan aikin tsaro da tallafin ayyukan wanzar da zaman lafiya, sai dai wasu keɓantattun shirye-shirye.
Dokar ta kuma hana bayar da lasisin sayar da kayan aikin soji kai tsaye ga waɗannan ƙasashe.
Rahoton ya kuma bayyana cewa babu wani jami’in gwamnati da aka gurfanar a gaban kotu saboda hannu a fataucin mutane, duk da zarge-zargen cin hanci da rashawa.
A lokaci guda, adadin waɗanda gwamnati ta taimaka wa bayan sun tsira daga fataucin mutane ya ragu daga 2,058 a shekarar da ta gabata zuwa mutum 675.
Dangane da matakan tabbatar da doka, rahoton ya ce hukumomin Najeriya sun gudanar da bincike kan shari’o’in fataucin mutane 1,341, cewar Daily Post.
Daga cikin waɗannan shari’o’i, 589 sun shafi fataucin mutane domin lalata, 301 sun shafi aikin dole, yayin da 451 ba a fayyace nau’in laifin ba. Shari’o’in sun shafi mutum 1,367 da ake zargi.
Boko Haram, ISWAP na amfani da yara kanana
Rahoton ya bayyana Boko Haram da ISWAP a matsayin ƙungiyoyin da ke ɗaukar yara da amfani da su a ayyukan yaƙi.
Ya ce ƙungiyoyin na ci gaba da ɗaukar yara, sace su da amfani da su ta hanyar ƙarfi, yaudara ko tilastawa.
Yaran, waɗanda shekarunsu za su iya kai 12, ana amfani da su a matsayin masu dafa abinci, masu aikin gida, ’yan leƙen asiri.
Trump ya rubuta wasika ga Tinubu
A baya, an ji cewa Donald Trump na Amurka ya yaba wa shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu kan jajircewarsa wajen yaki da ’yan ta’adda.
Shugaban na Amurka ya ce dangantakar Amurka da Najeriya na da muhimmanci wajen yaki da ta’addanci.
Asali: Legit.ng


