Aikin noma
Manoma a jihar Bauchi sun bayyana cewa karin kudin wutar lantarki da cire tallafin mai da Bola Tinubu ya yi ne suka jawo tsadar tumatur a kasuwannin Najeriya.
Gwamnatin tarayya ta bayyana matakan da ta dauka domin shawo kan matsalar hauhawar farashin abinci a Najeriya. Ministan noma Abubakar Kyari ne ya fadi haka.
Ƴan bindiga sun gindaya sharuda ga wasu manoma a yankin Unguwar Jibo da Nasarawa da ke karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna kan laifuffukan da suka aikata.
Ma’aikatar albarkatun noma da wadata kasa da abinci ta gargadi ‘yan Najeriya kan bullar wata cuta a jikin dabbobi a kasuwar dabbobi ta jihar Kwara.
Gwamnatin tarayya ta fara raba kayan tallafin noma ga manoma daga shiyyoyi uku na jihar Kano a wani yunkuri na habaka samar wa kasa abinci da habaka noma.
Yawaitar ayyukan ta'addaci sun jawo manoma da dama sun kulle gonakinsu a Arewacin Najeriya wanda hakan yasa masana hasashen samun karancin abinci.
Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta kara raba tallafin kayan abinci ga mazauna jihar ba. Ya ce kowa ya koma gona.
An yi kyakkyawar hadaka tsakanin gwamnatin tarayya da jihar Enugu inda aka fara noman rogo tare da sarrafa shi zuwa sinadarin man fetur. Yanzu shirin ya yi nisa.
Babban bankin kasa CBN ya bukaci bankunan kasuwanci a jihar Kano da su shiga cikin tsarin nan na bada bashin noma domin bunkasa fannin noma a kasar nan.
Aikin noma
Samu kari