IMF: Falana Ya Fadi Wadanda Suka 'Ingiza' Gwamnatin Najeriya ta Kara Kudin Wuta

IMF: Falana Ya Fadi Wadanda Suka 'Ingiza' Gwamnatin Najeriya ta Kara Kudin Wuta

  • Lauya Femi Falana SAN ya zargi bankunan IMF da WB da zuga gwamnatin Najeriya wajen tsawwala farashin wutar lantarki
  • Shahararren lauyan na wannan batu ne bayan karin kudin wutar lantarki, a lokacin da wutar kuma ta yi karancin a sassan Najeriya
  • Ya zargi gwamnatin Najeriya da gaza kare muradun al'ummarta, duk da kasashen da ke ingiza ta na yi wa al'ummarsu ayyukan raya kasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Lagos-Shahararren Lauyan nan mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Femi Falana SAN ya zargi bankin lamuni na duniya (IMF) da bankin duniya (WB) da ingiza Najeriya wajen kara kuntatawa al'ummarta.

Kara karanta wannan

Karin kudin lantarki: Majalisar wakilai ta ba hukumar NERC sabon umarni

Lauyan ya ce gwamnatin Najeriya ba ta iya kare yan kasarta, ya na mai cewa karin kudin wutar da gwamnatin tarayya ta yi, kare muradun bankunan biyu ne kawai.

Lauyan na ganin shugabannin Najeriya sun zama yan amshin shata
Femi Falana ya ce Najeriya ba ta da muradun kanta Hoto:@femi_falana
Asali: Twitter

Falana, Tinubu, IMF da bankin Duniya

A wata hira da ya yi a cikin shirin Politics Today na tashar Channels Television, lauya Femi Falana ya ce ministan harkokin wuta na aiwatar da bukatun da IMF da bankin duniya su ka tsara masa ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Falana ta kara da cewa hukumar wutar lantarki ta NERC da Ministan harkokin wutar ba za su iya nunawa yan Najeriya komai a kasa ba duk da karin kudin wutar.

"Amurka na da fuskar biyu," Falana

Shahararren lauyan ya zargi Amurka da kawayenta da baki biyu domin su na hana Najeriya ayyukan ci gaban al'ummarta.

Kara karanta wannan

Lantarki: Minista ya fadi masifar da za a shiga idan ba a kara kudi ba, ya yi gargadi

Ya ce a kasashen Amurka da kawayenta, ana bayar da tallafi a bangaren noma da makamashi sannan su na bawa dalibansu bashi.

Lauyan ya yi takaicin yadda kasashen ke hana shugabannin Najeriya aiwatar da ayyukan da su ke yi wa al'ummarsu a kasar nan, kamar yadda vanguard ta wallafa.

A cewar Falana, sam bai dace hukumomin kasar nan su nemi a biya su kuɗin wutar da ba sa samarwa ba.

"A janye karin kudin wuta," Majalisa

A baya mun kawo mu ku cewa majalisar wakilai ta nemi hukumar kula da wutar lantarki ta kasa (NERC) ta gaggauta janye karin kudin wutar da ta yi a baya.

A zamanta na ranar Talata, majalisar ta bayyana cewa za ta nemi a rangwantawa jama'a halin da su ke ciki ta cikin wani kudiri mai muhimmanci ga jama'a da yan majalisa su ka amince da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel