Uwargidar Shugaban Kasa Remi Tinubu ta Kaddamar da Shirin Noma ga Mata a Arewa

Uwargidar Shugaban Kasa Remi Tinubu ta Kaddamar da Shirin Noma ga Mata a Arewa

  • Mai dakin shugaban Kasa, Sanata Remi Tinubu ta kaddamar da shirin noma na gwamnatin tarayya ga mata a Arewa ta tsakiya
  • Sanata Remi Tinubu ta bayyana cewa gwamnati na sane da muhimmancin manoma mata wajen ciyar da kasar nan gaba
  • An rarraba Naira miliyan goma ga kowace jiha domin bata damar tallafawa matan su yi nomansu da gaske

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jos- Uwargidar Shugaban kasa, Remi Tinubu ta kaddamar da shirin noma ga matan dake yankin Arewa ta tsakiya, inda ta bayyana cewa an raba naira miliyan 10 ga jihohin domin tallafawa manoman.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnatin tarayya ta fara bayar da tallafin N50,000 ga mutanen Najeriya

Da take kaddamar da shirin noman a Jos a Talatar nan, Remi Tinubu ta ce yanzu haka ana gudanar da shirin a sauran sassan kasar nan.

Remi Tinubu
Uwargidar Shugaban Kasa Remi Tinubu ta Kaddamar da Shirin Noma ga Mata a Arewa Hoto: Excellency Remi Tinubu
Asali: Facebook

Remi Tinubu wacce ta samu wakilcin matar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Salamatu Gbajabiamila ta ce a Kudancin kasar nan ne kawai ba a fara shirin noman matan ba, kamar yadda The Cable ta ruwaito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nawa Remi Tinubu ta rabawa mata manoma?

Mai dakin shugaban kasar ta bayyana cewa sun shirya tallafawa matan da kudi a jihohin dake yankin Arewa ta tsakiyar domin bunkasa noma.

Ta ce gwamnatin da mai gidanta ke jagoranta tana sane da muhimmancin noman matan ga tattalin arzikin kasa.

Saboda haka ne aka warewa kowacce jiha a yankin Naira miliyan 10 da ake sa ran rabawa ga mata 20.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An yi wa yarinya 'yar shekara 10 kisan gilla a wani birnin Arewacin Najeriya

Jihohin da aka ba kudin sun hada da Neja Nasarawa, Filato, Kwara da Kogi, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

A Kalamanta:

“Wadannan namoma ne ta fannin noma, kiwo, kiwom tsuntsaye da noman kifi. Nan gaba kadan, sabon shirin gwamnatin tarayya hadin gwiwa da ma’aikatar gona za ta tallafawa manoma.”
“A yanzu haka muna gudanar da shirin a shiyyoyin kasar nan uku. A Arewa ta Gabas- Borno; a Arewa maso yamma-Kebbi; a kudu maso yamma- jihar Ogun; za mu sanar da lokacin da za a kaddamar da shirin a kudu maso kudu nan gaba.”

Gwamnati za ta tallafawa manoma

A bayan nan gwamnati a jihar Katsina ta tallafawa manoman jihar sama da dubu biyu da kayan noma domin bunkasa noman rani a jihar, kamar yadda Gwamna Dikko Radda ya tabbatar.

Gwamna Dikko Radda ya ce an yi hakan ne domin taimakawa manoman rani wajen wadata jihar da kayan abinci, kuma an bayar da kayan noman ne kyauta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel