Farashin Shinkafa Ya Fara Sauka Bayan Azumi a Kasuwannin Arewa

Farashin Shinkafa Ya Fara Sauka Bayan Azumi a Kasuwannin Arewa

  • Bincike ya nuna an fara samun saukar farashin shinkafa a kasuwannin Arewacin Najeriya cikin satin da ya wuce zuwa yanzu
  • Binciken ya tabbatar da cewa duk da an samu sauƙin farashin, amma akwai bambancin farashi a tsakanin kasuwanni dake fadin Arewacin kasar
  • Legit ta tattauna da Aminu Abubakar, wani mai kasuwancin shinkafar buntu a Arewa maso gabas domin jin yadda farashin yake a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an fara samun saukar farashin shinkafa a kasuwannin jihohin Arewa.

Sai dai a mafi yawan kasuwannin, binciken ya shafi farashin shinkafar buntu ne.

Rice and goods
Yan Najeriya sun nuna farin ciki da fara samun saukar farashin shinkafa. Hoto: Getty image
Asali: Getty Images

A shekarun baya, buhun shinkafar buntu ba ya wuce N9,000 zuwa N20,000.

Kara karanta wannan

29 ga Mayu: Abubuwan da gwamnati ta shirya yi a bikin cikar Tinubu shekara 1 a mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma daga shekarar 2023 zuwa shekarar da mu ke ciki, farashin ya haura tsakanin N55,000 zuwa N70,000

A wani bincike da jaridar Daily Trust ta fitar, ya nuna cewa an fara samun sauƙin farashin shinkafar a mafi yawancin kasuwannin Arewa.

Farashin shinkafa daga kasuwannin Arewa

A jihar Kebbi an samu saukar farashin shinkafar musamman a yankunan da ake noma.

A yankunan da ba a noma, farashin ya kai N50,000 zuwa N55,000 a buhu mai nauyin kilo 100. Amma a yankunan da ake noma kamar Aljanari da Suru farashin yana kan N43,000 zuwa N45,000.

Haka an samu raguwar farashin a yankin Birnin Kebbi da Argungu A jihar Neja, an samu saukar farashin shinkafar.

'Yan kasuwa da manoma sun tabbatar da ana samun buhun shinkafar daga N49,000 zuwa 42,000 a buhu mai nauyin kilo 100.

Kara karanta wannan

Kwamishinoni sun ba hammata iska a taron karbar sababbin tuba daga PDP zuwa APC

Haka labarin ya ke a jihar Jigawa. An tabbatar da saukar farashin a kasuwar Larabar Tambari Gwani da ke karamar hukumar Dutse.

A kasuwar, an samu farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 100 a kan N55,000 a ranar Laraba. Amma kafin ranar, ana sayar da buhun ne akan N60,000

A jihar Taraba ma an samu saukar farashin. Rahotanni sun tabbatar da cewa buhu mai nauyin kilo 100 ana samunsa a kan N40,000 wanda a satin da ya wuce yana kai N50,000

A jihar Katsina, rahoton ya ce an samu labarin saukar farashin. Farashin ya sauko daga tsakanin N55,000 da 60,000 zuwa N40,000 da N54,000.

Haka aka samu labarin a jihar Kano, amma sai dai a nan kam saukar farashin ya shafi shinkafar gwamnati ne.

Rahotanni sun tabbatar da cewa farashin shinkafa 'yar Thailand ya ragu daga N87,000 zuwa N66,500 a kan buhu mai nauyin kilo 50.

Kara karanta wannan

Taushen Fage: Al'adar cin nama da sada zumunta da ta shekara sama da 100 a Sakwaya

Dalilan saukar farashin shinkafa

Manoma da dama da masu sayar da shinkafa sun bayyana dalilai da dama a kan dalilin saukar farashin.

Wasu sun jingina saukar farashin ne da saukar dala da ake cigaba da samu kwannan. Wasu kuma suka jingina samun sauƙin da shigowar shinkafar da aka noma a rani.

A wani bangaren kuma, wasu sun ce dalilin sauƙin shi ne a halin yanzu manoma na fito da shinkafar kasuwa domin samun kudin da za su yi nomar damina.

Hirar Legit da mai sayar da shinkafa

Yayin da Legit ta tattauna da Aminu Abubakar, wani mai harkar shinkafa a Arewa maso gabas, ya tabbatar da saukar farashin shinkafa a jihar Adamawa.

Ya ce, a garin Tinno na jihar Adamawa a halin yanzu ana samun buhun shinkafar buntu a N35,000 zuwa N36,000 alhali a kwanakin baya farashin yana tsakanin N43,000 zuwa 45,000.

A cikin hirar, ya jingina dalilin saukar farashin ne da samuwar yawan shinkafar da aka noma a rani.

Kara karanta wannan

Tinubu ya magantu bayan Dangote ya rage farashin mai, ya ja hankalin 'yan Najeriya

An yi hasashen saukar kayayyaki Najeriya

A wani rahoton kuma, kun ji cewa sabon nazarin asusun bada lamuni na duniya (IMF) ya yi hasashen samun saukar farashin kayayyaki a faɗin Najeriya a cikin shekaru masu zuwa.

Hasashen ya kuma kara nuni da cewa za a samu haɓakar tattalin arzikin kasar cikin shekaru masu zuwa saboda wasu matakai da gwamnatin kasar ke dauka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel