'Akwai Manyan da ke yi wa Gwamnatina Makarkashiya', Gwamnan APC Ya Koka

'Akwai Manyan da ke yi wa Gwamnatina Makarkashiya', Gwamnan APC Ya Koka

  • Gwamnatin jihar Kebbi ta zargi wasu manyan jihar da kokarin yi masu makarkashiya a kokarinsu na inganta rayuwar mazauna jihar ta fuskoki da dama
  • Mai girma Nasir Idris ne ya bayyana hakan a taron bikin gargajiya da nuna kayan noma na Uhola da ake gudanarwa a Zuru, inda ya ce wasu na yi masa katsalandan
  • Dr. Nasir Idris ya ce ba za su girgiza ba duk da shigar masa aiki da kokarin kawo tsaiko ga ayyukan ci gaban da gwamnatinsa ke son kawowa jihar Kebbi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kebbi- Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris ya yi zargin wasu manyan jihar na yiwa gwamnatinsa makarkashiya.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta dawo da lantarki a garuruwan da aka yi shekaru babu wuta a Sokoto

Ya ce amma gwamnatinsa a tsaye ta ke wajen kare muradun 'yan jihar da ciyar da su gaba, ta fuskokin da su ka dace.

Gwamna Nasir Idris
Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi ya zargi wasu a jiharsa da yiwa gwamnatinsa makarkashiya Hoto: Nasir Idris Kauran Gwandu
Asali: Facebook

A rahoton da Daily Trust ta wallafa, Gwamnan Kebbi ya bayyana zargin ne a taron bikin gargajiya na Uhola da nuna kayan noma a Zuru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wasu sun hana aikin titin Zuru," Gwamna

Gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa ya gano wasu sun je ma'aikatar ayyuka a Abuja tare da yin kulla-kulla wajen musanya takardar neman gina titin Koko Dabai da na Bui-Kangiwa-Kamba da ya tafi zuwa iyakar jamhuriyar Nijar.

A kalamansa:

"Titin Koko-Dabai na bukatar kulawar gaggawa fiye da titin Bui-Kamba wanda mutane ke iya bi a halin yanzu."

Dr. Nasir Idris ya ce da takaici sosai idan ya ga halin da titunan zuru ke ciki, kamar yadda Nairaland ta wallafa.

Kara karanta wannan

Mai dokar bacci: mazauna Kano sun zargi sojan sama da kashe dan uwansu

Ya yi alkawarin hada kan iyayen kasa da ke masarautar Zuru dasShugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu domin nemawa al'ummar yankin mafita.

Gwamnan ya kara da alkawarin daukar nauyin bikin Uhola duk shekara saboda muhimmancinsa wajen hada kan mutanen jihar.

Gwamna Nasir ya raba tirelolin abinci

A baya kun samu labarin cewa Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi zai raba tireloli 200 na abinci ga mazauna jihar, saboda kawo sauki cikin halin matsin da su ke ciki.

Haka kuma gwamnan ya ce matakin raba tirelolin abincin somin-tabi ne wajen taimakawa mutanen da ya ke jagoranta, inda ya bayyana raba injunan ruwa ga manoma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel