Aikin noma
Gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu, ta karbo aron ¥15bn daga wata hukumar ƙasaar waje domin bunkasa harkar noma a Najeriya, sai an shekara 30 ba a gama biya ba.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci gwamnonin jihohin kasar nan da su samar da filayen kiwo ga makiyaya don kawo karshen rikicinsu da manoma.
Majalisar wakilai ta ce rashin tsaro da aka dade ana fama da shi a yankin Arewa maso Gabas da sauran sassan Najeriya ya jawo karancin samar da abinci a kasar.
An gano fasa kwauri da ambaliya a matsayin musabbabin karancin abinci da tsadar rayuwa. Wannan dai na fitowa daga gwamnatin Najeriya ta bakin ministan noma.
Jama’an gari sun sace abinci da aka tarwatsa wurin ajiyan kaya a birnin Abuja. Bisa dukkan alamu jami’an tsaro ba su ankara da wuri ba ko kuwa ba a iya kai dauki ba.
Yayin da ake shan fama da tsadar abinci a Najeriya, Gwamnatin Tarayya ta yi magana kan lokacin da za ta fara rabon kayan hatsi na tan dubu 42 a jihar Neja
Mun kawo labarin inda aka kwana game da alkawarin raba kayan abinci saboda ana yunwa. An tanadi metric 42, 000 a cikin 102, 000, za a fara rabawa talakawa.
Ministan tattalin arzikin kasa, Olawale Edun ya ce farashin abinci zai fado. Gwamnatin tarayya za ta raba buhuna 1, 407,205 domin farashin abinci ya sauko.
A lokacin da ake neman abinci a Najeriya, sai ga motoci za su tsallaka Nijar. Mai magana da yawun bakin hukumar ZARTO a Zamfara ya tabbatar da wannan zance.
Aikin noma
Samu kari