Layyah: Ana Shirin Babbar Sallah, Gwamnati na Yiwa Jama'a Gargadin Guba a Jikin Dabbobi

Layyah: Ana Shirin Babbar Sallah, Gwamnati na Yiwa Jama'a Gargadin Guba a Jikin Dabbobi

  • Gwamnatin tarayya ta tabbatar da guba a jikin wasu dabbobi a kasuwar Mandate dake jihar Kwara wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wasu daga dabbobin
  • A rahoton da ma'aikatar ta fitar, ta ce an gano cewa dabbobin sun ci guba ne a wurin da suka yi kiwo, kuma hakan illace ga su da masu sayen nama
  • Ta bayyana cewa tuni aka dauki matakan ba dabbobin da suke raye magani, sannan ana tsaftace mayankar Mandate tare da wayar da kan jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kwara- Ma’aikatar albarkatun noma da wadata kasa da abinci ta gargadi ‘yan Najeriya kan bullar guba a jikin dabbobi a kasuwar dabbobi ta 'Mandate' dake Ilorin a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya kafa kwamitin bincike saboda yawan faduwa jarrabawar 'qualifying'

Wannan gargadi na zuwa ne yayin da musulmi ke shirye-shiryen gudanar da bikin sallar layya nan da kwanaki 26.

Raguna
Ana shirin bikin sallah babba, an gano guba a jikin dabbobi Hoto: Utomi Pius Ekpei
Asali: Getty Images

Dabbobi sun kamu da cuta

Rahoton da ma’aikatar albarktun noma ta fitar, ta tabbatar da mutuwar dabbobi da dama a ranar 20 ga watan Afrilu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sakamakon binciken da ta wallafa a shafinta, ma'aikatar ta ce sun gano dabbobin sun ci abincin da aka yiwa feshin magani, wanda hakan ne ya jayo asarar rayukansu.

'Akwai likitocin dabbobi a kasa' - Gwamnati

Bayan tabbatar da guba a jikin wasu dabbobi dake kasuwar 'Mandate' a jihar Kwara, gwamnati ta bayyana cewa akwai likitocin dabbobi a kasa.

Nigerian Tribune ta wallafa cewa dama gwamnati ta samar da irin wadannan likitocin ko-ta-kwana domin tunkarar irin wannan matsala.

Rahoton ya kara da cewa an baya dabbobi kimanin 40 magani, kuma alamu sun nuna cewa suna samun lafiya sosai.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani game da hatsarin jirgin sama da ya kashe shugaban Iran

Ma'aikatar ta kara da cewa ta dauki matakan tsaftace kasuwar, tare da wayar da kan al'umma domin gujewa ta'ammali da nama mai guba.

An tsawaita hutun sallah a Gombe

A baya mun baku labarin cewa gwamantin jihar Gombe ta tsawaita hutun karamar sallah zuwa ranar domin gudanar da bukukuwan sallah cikin nishadi.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ne ya tsawaita hutun sallar wanda rahotanni su ka ce ba zai rasa nasaba da hawan sallah da ake yi na kwanaki uku a jihar ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel