Farin Ciki a Jihar Arewa Yayin da Farashin Shinkafa Ya Karye Daga N60, 000

Farin Ciki a Jihar Arewa Yayin da Farashin Shinkafa Ya Karye Daga N60, 000

  • A yayin da 'yan Najeriya ke kuka tsadar rayuwa, a hankali ana farashin kayayyaki musamman na abinci na karyewa a kasar
  • Na baya bayan nan shi ne karyewar farashin buhun shinkafa a jihar Kwara, inda a yanzu ake sayar da kilo 50 kan N52,000 zuwa N54,000
  • A cewar 'yan kasuwa, nan da makonni shinkafar na iya komawa kasa da N30,000, lamarin da ya jefa farin ciki a zukatan mazauna Ilorin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Da yawan mazauna jihar Kwara na nuna farin ciki yayin da buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 ya koma tsakanin N52,000 zuwa N54,000.

Farashin shinkafa ya karye zuwa N52,000 a Ilorin, jihar Kwara
'Yan kasuwa sun yi albishir da cewa shinkafa za ta iya kai wa kasa da N30,000 nan gaba kadan. Hoto: Bloomberg / Contributor
Asali: Getty Images

Farashin ya karye ne daga Naira 80,000 da aka sayar da ita a cikin watan Ramadan a kasuwannin da ke fadin Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Za mu hukunta masu boye kaya, Shugaban kasuwa zai yaki tashin farashin abinci

Naira ta kara karya farashin shinkafa

Yawancin mazauna birnin na Ilorin, waɗanda suka yi magana da jaridar Daily Trust sun nuna tsantsar jin dadinsu kan wannan ragi da aka samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kasuwar Mandate da ke Ilorin babban birnin jihar, masu sayar da hatsi da kayan abinci sun tabbatar da cewa an samu raguwar farashin kayan abinci musamman shinkafa.

Da yawa daga cikin ‘yan kasuwar sun danganta lamarin da yadda Naira ta kara karfi a kan Dala a makonnin da suka gabata, da dai sauransu.

"Shinkafa za ta karye zuwa 30,000" - AbdulAfeez

Fasto Adeyanju Adeyemo, wani dillalin shinkafa, ya ce a hankali farashin shinkafar kasar waje yana raguwa, musamman ga wadanda suke saye da kudin kasashen waje.

Adeyemo ya ce:

“A makon da ya gabata, an sayar da ita a kan N61,000, amma yanzu tana a kan N54,000, kuma na shaida wa abokan hulda na cewa idan har aka ci gaba da tafiya a hakan, nan da wata daya za ta koma N25,000."

Kara karanta wannan

Tinubu zai karbo sabon bashin Dala biliyan 2.25 daga bankin duniya

Mista Abdullateef AbdulAfeez, wani mai sayar da shinkafa ya ce:

“Yanzu muna sayar da N50kg a kan Naira 52,000, da hasashen za ta koma N30,000 a cikin ‘yan makonni kadan la'akari da halin da ake ciki a yanzu."

Mazauna Ilorin na murnada saukin shinkafa

Sai dai Abubakar Ibrahim ya ce farashin kayan abincin da ake nomawa a cikin gida bai yi kasa ba saboda kalubalen tsaro.

Misis Adesanmi Temilola, wata kwastoma, yayin da take bayyana jin dadin ta game da ci gaban da aka samu, ta ce ana samun tafiyar hawainiya a ragin kudin idan aka kwatanta da lokacin da Dala ke tashi.

Da yawa daga cikin mazauna yankin sun bayyana farin cikinsu da wannan sabon ci gaban, inda suka roki gwamnati da cewa ta kawo tsare-tsare da za su kara karya farashin kayan abinci.

"Dizal zai karye zuwa N700" - IPMAN

A wani labari kuma, Legit Hausa ta ruwaito kungiyar dillalan mai ta kasa (IPMAN) ta yi albishir da cewa farashin man dizal zai karye zuwa N700 nan gaba kadan.

IPMAN ta bayyana hakan ne yayin da take yabawa kokarin mamatar man Dangote na karya farashin dizal zuwa N1,000 daga N1,2000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel