Rashin Tsaro: Karancin Noma a Arewa Na Barazanar Kawo Matsalar Abinci a Najeriya

Rashin Tsaro: Karancin Noma a Arewa Na Barazanar Kawo Matsalar Abinci a Najeriya

  • Ana hasashen raguwar abinci a Najeriya saboda yadda ayyukan ta'addanci suka jawo aka daina noma a yankuna da dama
  • Manoma da dama sun koka kan yadda ayyukan yan bindiga da masu garkuwa da mutane suka tilasta musu daina noma a Arewa
  • Sai dai gwamnatin tarayya ta bayyana wani mataki da za ta dauka cikin gaggawa domin ganin lamarin bai kai ga yin tasiri ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Ana hasashen samun karancin abinci saboda rufe gonaki da dama da aka yi a yankunan Arewacin Najeriya.

Manoman Arewa
Matsalar tsaro na barazana ga ayyukan noma a Arewa. Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Luis Tato
Asali: Facebook

An rage zuwa gona a Arewacin Najeriya

An daina noma a manyan gonaki da aka saba musamman wadanda suke hanyoyin Zamfara, Kaduna, Abuja, Lokoja da sauransu.

Kara karanta wannan

Ana tsoron rikici kan tukunyar miya ya jawo asarar rayuka a birnin Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Binciken Daily Trust ya nuna cewa daina noma a gonakin yana da alaka ne da yawaitar ayyukan ta'addanci da na 'yan bindiga.

Halin da manoma suka shiga a Arewa

Wani dan majalisar jihar Kaduna da yake da gona a Birnin Gwari ya ce ya rufe gonarsa saboda ayyukan yan bindiga a yankin.

Dan majalisar ya ce a baya ya kasance yana ziyartar gonar a kai-a kai yana duba masu aiki amma a yanzu babu halin zuwa saboda rashin tsaro.

Haka zalika wani manomi da ke da gona a kan hanyar Kaduna zuwa Niger, Hussaini Udawa, ya ce ya daina aikin gona saboda rashin tsaro.

Malam Hussaini ya ce rufe gonar ya jawo ma'aikata da dama sun rasa ayyuka domin a shekara yana noma buhu 500.

Wata ma'aikaciyar gwamnati mai suna Mairo Ahmadu ta ce mahaifin ta ya hakura da gonarsa a jihar Sokoto saboda rashin tsaro.

Kara karanta wannan

"An yi amfani da bam": Mutum 1 ya mutu da aka bankawa masallata wuta a Kano

Ta ce a gonar suna noma tare da kiwon shanun madara amma a halin yanzu babu damar yin haka.

Jawabin shugaban kungiyar manoma a Najeriya

Shugaban kungiyar manoma ta kasa (AFAN), Kabiru Ibrahim ya ce lallai ayyukan ta'addanci sun yi tasiri a harkokin noma a Arewacin Najeriya.

Shugaban ya kuma yi kira ga gwamnati wurin daukan matakin da ya dace domin ganin manoma sun dawo gonakinsu.

Masana harkar noma sun hango barazana

Wani masanin harkokin noma, Amos Banda ya ce yawancin wuraren da aka samu matsalar yankuna ne da suke samar da abinci sosai.

Saboda haka ake ganin akwai barazana ga harkar samar da abinci a Najeriya idan ba a dauki mataki ba.

Sai dai a nata bangaren, gwamnatin tarayya ta yi alkawarin samar da jami'an tsaro na musamman a gonaki.

Kungiyar manona ta yabi Tinubu

A wani rahoton kun ji cewa Kungiyar Manoma a Najeriya (AFAN) ta yabawa shugaban kasa, Bola Tinubu kan matakin kwato kudin noma da gwamnati ta raba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: 'Rashin tsaro a Arewa zai haifar da babbar fitina a yammacin Afrika', gwamna

Sai dai kungiyar ta ce an tafka kuskure wurin yin rabon don ba manoma ba ne su ka ci kudin kuma hakan ya biyo bayan rashin bin tsari ne tun a karon farko.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel