Shugaba Tinubu Ya Karbo Sabon Bashin Biliyoyi, Minista Ya Fadi Inda Za a Jefa Kudin

Shugaba Tinubu Ya Karbo Sabon Bashin Biliyoyi, Minista Ya Fadi Inda Za a Jefa Kudin

  • Gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu, ta karbo aron ¥15bn daga wata hukumar ƙasar waje domin bunkasa harkar noma a Najeriya
  • An ruwaito cewa an karbo kudin ne daga hukumar ƙasa-da ƙasa ta Japan, wanda ya kai ƙimar N138,080,879,820 a lissafin kuɗin Najeriya
  • Ministan harkokin kuɗi da tattalin arziki na kasa, Wale Edun ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu, ta karbo aron ¥15bn daga hukumar ƙasar waje domin bunkasa harkar noma a Najeriya.

Ministan Tinubu ya yi magana kan N138bn da Najeriya ta ranto daga Japan
Najeriya za ta yi amfani da ¥15bn da ta karbo daga Japan wajen bunkasa harkar noma: @officialABAT, @FinMinNigeria
Asali: Twitter

The Cable ta ruwaito cewa an karbo kudin ne daga hukumar ƙasa-daƙasa ta Japan, wanda ya kai ƙimar N138,080,879,820 a kuɗin Najeriya.

Kara karanta wannan

Kano: Daina amfani da soshiyal midiya da wasu sharuɗa da kotu ta kafawa Murja Kunya

Za a biya bashin shekara 30

Jaridar ta ce ministan kuɗi da tattalin arziki, Wale Edun ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Najeriya za ta biya bashin ne a cikin shekaru 30, amma ba za ta fara biya ba sai bayan shekara 10 da karbar kuɗin, kuma za ta biya kudin ruwa na kaso 10.

Ministan ya ce babu wata yarjejeniyar bayan fage da gwamnati ta yi da kasar Japan kafin ta karbi aron kudin.

Tinubu ya kafa kwamitin EMT

Rahoton jaridar The Nation ya nuna cewa majalisar zartarwar Najeriya, ta amince da kafa kwamitin tattalin arziki (EMT).

A cewar ministan kuɗi, kwamitin zai yi aiki ne domin kawo hanyoyin bunkasa tattalin arziki, samar da ayyuka da rage talauci a ƙasar.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya shiga sabuwar matsala kan zargin alaƙa da ƴan bindiga, bayanai sun fito

Edun ya ce nan da watanni shida, kwamitin zai shawo kan dukkan matsalolin da aka samu a kasafin kudi da tabbatar da daidaitar lamura.

SERAP na so a binciki gwamnatin Buhari

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa SERAP ta nemi gwamnatin Bola Tinubu da ta binciki inda aka kai $3.4bn da gwamnatin tsohon shugaban kasa Buhari ta karbo.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, SERAP na zargin cewa bashin da aka karbo daga wajen hukumar IMF ba a yi aikin komai da shi ba, kuma ba a san yadda aka yi da kudin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel