Bola Tinubu Ya Fadawa Gwamnoni Mafita Game da Rikicin Manoma da Makiyaya

Bola Tinubu Ya Fadawa Gwamnoni Mafita Game da Rikicin Manoma da Makiyaya

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gano hanyar da za a kawo ƙarshen rikicin makiyaya da manoma a Najeriya
  • Shugaba Tinubu ya buƙaci gwamnonin jihohin ƙasar nan da su samar da filayen yin kiwo ga makiyaya
  • Shugaban ƙasan ya koka kan illar da rikicin makiyaya da manoma ke yi wajen yunƙurin samar da abincin da zai wadaci al'ummar ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci gwamnonin jihohi su samar da filayen kiwo ga makiyaya.

Jaridar Daily Trust ta ce shugaban ƙasan ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin, 11 ga watan Maris, a yayin wata ziyarar ƙaddamar da wasu ayyuka da ya kai a jihar Neja.

Kara karanta wannan

"Ka da ka zama kamar Buhari": An ba Tinubu shawarar magance matsalar rashin tsaroS

Tinubu ya yi kira ga gwamnoni
Shugaba Tinubu ya bukaci gwamnoni su samar da filayen kiwo ga makiyaya Hoto: @OfficialABAT
Asali: Facebook

Kiran da shugaba Tinubu ya yi

Tinubu ya ce samar da filayen kiwo ga makiyaya zai kawo ƙarshen rikicin da aka daɗe ana yi tsakanin manoma da makiyaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan rikici ya jawo asarar rayuka da amfanin gona kamar yadda rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Ya kuma buƙaci gwamnonin da su biya ma’aikata ƙarin albashi domin ciro jama'a daga halin yunwa da ƙuncin rayuwa.

Wace buƙata Tinubu ya nema a wajen gwamnoni?

A kalamansa:

"Dole ne ku kula da jama’armu, kuma ku sake farfaɗo da noma ciki har da shirin kiwo. Ban ga dalilin da ya sa Najeriya ba za ta iya ciyar da dukkan ɗaliban da ke makarantunmu da lita ɗaya ta madara a kowace rana ba idan an yi amfani da tsarin kiwo mai kyau.
"Na san abin da hakan ke nufi a matsayin zagon ƙasa ga tattalin arziƙi idan shanun da ke yawo suka cinye amfanin da ke gonakinmu. Abin akwai ciwo amma idan muka wayar da kan makiyaya tare da samar da wuraren kiwo, za a kawar da matsalar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fayyace gaskiya kan masu zargin Buhari ne ya lalata Najeriya

"Gwamnoni su samar da filayen, ni kuma a matsayina na shugaban ƙasa, na ƙuduri aniyar ba ku cikakken shirin da zai magance wannan matsala ta hanyar korar yunwa daga doron ƙasa.”

Ayodele ya faɗi illar makiyaya da ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban cocin INRI, Primate Elijah Babatunde Ayodele ya ɗora alhakin halin da ƙasar nan ke ciki kan ayyukan kashe-kashe da ƴan ta'adda da makiyaya.

Babban faston ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta aiwatar da hukuncin kisa kan miyagun da aka samu da aikata irin waɗannan laifukan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel