Al'ummar Benuwai sun Shiga Rudani Bayan Makiyaya sun Kashe Mutum 3

Al'ummar Benuwai sun Shiga Rudani Bayan Makiyaya sun Kashe Mutum 3

  • Manoma sun shiga fargaba a jihar Benuwai bayan harin makiyaya da ya tilastawa manoma kauracewa gonakinsu saboda fargaba
  • Maharan da ake zargin makiyaya ne sun kashe mutane 3 da ke aiki a gonakinsu a kananan kauyukan Entekpa da Idabi a jihar
  • Mahukuntan yankin sun nemi taimakon gwamanti wajen dakile hare-haren da ya addabe su na tsawon lokaci tare da aiki musu jami'an tsaro

Jihar Benue -Wani harin da wasu da ake zargin makiyaya ne su ka kai jihar Benuwai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 3.

Ana zargin makiyayan da kai harin kan wasu kauyukan manoma biyu a jihar, tare da kashe mutanen a gonakinsu.

Gwamnan jihar enue, Hyacinth Alia
Ana fargabar mahara sun kashe manoma uku a kan gonakinsu Hoto: Benue State Government
Asali: Facebook

An kashe mutanen ne a mabanbantan hare-hare a kauyukan Entekpa da Idabi a karshen mako, kamar yadda Channels Television ta samu tabbaci.

Kara karanta wannan

Ganduje: An sake bankado yadda tsohon gwamnan ya karkatar da N51.3bn, an gano dalili

An nemi tallafin gwamnati a Benuwai

Shugaban karamar hukumar Otukpo a jihar Benuwai, Alfred Omakwu ya tabbatarwa Channels cewa suna bukatar taimakon gwamnati wajen magance hare-haren makiyayan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an dade ana kai hare-hare, wanda ya sa manoma su ka kauracewa gonakinsu.

Alfred Omakwu ya kara da cewa sai da makiyayan su ka fara kai hari gonar wani manomi a Entekpa, sannan su ka kara gaba Adoka'Icho dake Idabi inda su ka kashe wasu mutum biyu.

"An dade ana kai hare-haren nan tun daga farkon kakar nan, amma muna rokon gwamnatin tarayya da ta jiha su gaggauta kawo mana dauki ta hanyar kawo mana jami'an tsaron da za su dakatar da hare-haren,"

- Shugaban karamar hukumar.

Ya kara da cewa duk da yanzu lokaci ne da ya kamata manoma su shiga gonaki domin shirin noma, amma fargaba ta hana su zuwa ko'ina. Rahotanni sun ce maharan sun kai hari a Otukpo, Apa, Agatu, Gwer West, Makurdi, Guma, Logo, Ukum, Kwande, da ke karamar hukumar Gwer ta gabas. Mutane 18 ne ake fargabar sun rasu a harin da maharan su kai garuruwan a ranar 7 ga watan Maris, 2024.

Kara karanta wannan

'Bam' da ƴan ta'adda suka dasa ya halaka bayin Allah sama da 10 a Arewacin Najeriya

Yan bindiga sun ka hari a Benuwai

A baya mun kawo mu ku yadda wasu yan bindiga su ka kai mummunan hari kauyen Ikoba a karamar hukumar Apa a jihar Benuwai.

Sun kashe mutum daya, yayin da mutane su ka shiga rudani baya da rahotanni su ka ce yan bindigar sun kona gidaje da dama a wani harin da aka fara kai wa kwana guda kafin wannan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel