Zaben Shugaban kasan Najeriya
Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta bayyana matsayarta game da yadda take shirin yin zaben 2023. Ta ce bata taba tunanin dage zabe ba, don haka za a yi zabe.
Gwamna Abdullahi Ganduje ya roki Kanawa su zabi Bola Tinubu, ya ce tun da mulki ya kasance a Arewa tun 2015, ya kamata yanzu ‘Dan Kudu ya zama shugaba kasa.
Muhammadu Buhari ya nuna hukumar INEC ba za ta canza lokacin zabe ba, shugaban kasa ya fadi haka da ya hadu fastoci a inuwar kungiyarsu ta CBCN a Aso Rock.
Wasu jam’iyyun siyasar da ba su da karfi za su goyi bayan takarar Atiku Abubakar. Sakataren yada labaran PDP a Najeriya ya ce sun dauko irin salon Bola Tinubu.
Gwamnatin kasar Birtaniya ta rufe kamfanin Next International mallakar tsohon gwamnan Anambra kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi.
Wasu daga cikin yan Nigeria na nuna shakkun su kan gadanar da babban zaben kasar nan da'a gudanar a watan gobe, inda za'a zabi sabon shugaban kasa da gwamnoni
A farkon nan Asiwaju Bola Tinubu ya zauna da Gwamnonin Jihohin APC da kwamitin da ke taya shi yakin zabe saboda a ga yadda za a shiryawa zaben shugabancin kasa.
Orji Uzor Kalu, bulaliyar majalisar dattawa ya ce Sanata Rabiu Musa Kwankwaso dan takarar shugaban kasa na NNPP da Peter Obi na jam'iyyar LP na yiwa Tinubu aiki
Babban malamin addini ya hango wanda zai gaji Buhari a zaben 2023, ya ce kowa ya yi hakuri, amma a nasa hange Atiku ne zai lashe zaben 2023 da ke tafe nan kusa.
Zaben Shugaban kasan Najeriya
Samu kari