Shekaru 15 Bayan Barin Mulki, Obasanjo Ya Fadi Abin da Ya Hana Shi Yin Tazarce Sau 2

Shekaru 15 Bayan Barin Mulki, Obasanjo Ya Fadi Abin da Ya Hana Shi Yin Tazarce Sau 2

  • Cif Olusegun Obasanjo yana ganin babu abin da ya isa ya hana shi kara zarcewa da ya nufin hakan
  • Tsohon shugaban Najeriyan ya ce bai taba yin niyyar ya nemi wa’adi na uku bayan Mayun 2007 ba
  • A game da zabe mai zuwa Obasanjo ya nuna ba da shi za a rika fita yawon yi wa Peter Obi kamfe ba

Ogun - Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya fito yana cewa da ya ga dama, da ya zarce a kan kujerar shugaban kasa bayan 2007.

Dazu Punch ta kawo rahoton da aka ji Cif Olusegun Obasanjo ya ce bai taba neman ya sake neman wani tazarce bayan kure wa’adinsa na mulki ba.

Sojan kasar yake cewa idan kuwa da ya so yin hakan, to da zai cigaba da mulki domin bai da ja da baya idan har ya sa wani lamari a gabansa.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Zauna da Fastoci a Aso Villa, Ya Fada Masu Gaskiyar Batun Ɗaga Zabe

Tsohon shugaban ya yi wadannan bayanai a wajen wani taro da kungiyar Africa Leadership Group ta shirya ta kafar yanar gizo a ranar Alhamis.

Obasanjo zai fita yawon kamfe?

A wannan zama da aka yi, Olusegun Obasanjo ya shaida cewa ba zai shiga tawagar yakin neman zaben Peter Obi ba, duk da yana goyon bayan shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dattijon ya ce ya yi iyakar abin da zai iya tun da ya rubuta takarda, yana nuna wanda yake goyon baya, jaridar The Guardian ta fitar da labarin nan dazu.

Obasanjo
Olusegun Obasanjo a wajen taro Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

“Ba na cikin tawagar yakin neman zabe. Nayi amfani da sanin aiki na, na fito karara nayi bayani.

Ba na cikin wata jam’iyyar siyasa, na fadi abin da shi ne ya fi dacewa da kasar nan.

- Olusegun Obasanjo

Da ake masa magana game da abin da ya kamata a duba wajen zaben shugaba, an rahoto shi yana cewa ayi la’akari da halayya, sanin aiki da dabi’a.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Kera Motar Wasan Tsere Da Hannunsa, Ya Tuka Ta a Hanyar Edo, Bidiyon Ya Yadu

Ban taba cewa ina so in yi wa’adi uku ba. Da ina neman wa’adi na ku, da na samu. Na san duk yadda zan bi domin in samu ko ta wani hali.

- Olusegun Obasanjo

Olusegun Obasanjo wanda ya yi mulki sau biyu bai yarda da masu sukar tsarin mulkin Najeriya ba, ya ce ba a rasa kura-kuran da za a iya gyara su.

Tinubu zai ci zabe - 'Dan majalisa

Rahoton da aka fitar ya ce Hon. Shamsudeen Danbazzau wanda ya yi ‘yan kwanaki a NNPP kafin dawowa APC ya fadi abin da zai nakasa PDP a 2023.

‘Dan majalisar wakilan tarayyar yake cewa Bola Tinubu zai doke ‘yan takaran 2023 a saukake, yana zaune a gefe guda NNPP da LP za suyi masa aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel