Saura ‘Yan Kwanaki a Shiga Zabe, Buhari Ya Aikawa Kasashen Waje Sako Na Musamman

Saura ‘Yan Kwanaki a Shiga Zabe, Buhari Ya Aikawa Kasashen Waje Sako Na Musamman

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya samu ganawa da wasu sababbin jakadun da aka tura zuwa Najeriya
  • Ganin zabe ya karaso, Buhari ya sanar da Jakadun su kula da aikinsu, su guji harka da bai shafe su ba
  • Kasashen Sudan ta Kudu, Thailand, Ireland Sanagal da Kudancin Sudan sun aiko sababbin Jakadunsu

Abuja - A yanzu ‘Yan Najeriya su na shirin zaben sabon shugaban kasa da wasu shugabanni a matakai dabam-dabam da hukumar INEC za ta shirya.

This Day ta ce ganin haka ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada kira ga Jakadun kasashen da ke Najeriya da su guji yi masu katsalandan.

A ranar Alhamis Muhammadu Buhari ya karbi wasikun Jakadun kasashen Switzerland, Suwidin, Jamhuriyyar Ireland, Thailand, Sanagal da Kudancin Sudan.

Da yake karbar wasikun a fadar shugaban kasa a birnin Abuja, mai girma shugaban Najeriyan ya yi kira ga sababbin jakadun da su maida hankali ga aikinsu.

Kara karanta wannan

Bishop Kukah Ya Magantu, Ya Fadi Abun da Babban Hadimin Buhari Ya Fada Masa Bayan Ya Caccaki Fadar Shugaban Kasa

Ban da shiga sharo-babu shanu

Kamar yadda Femi Adesina ya fitar da rahoto, Mai gidansa ya bukaci Jakadancin kasashen na ketare su takaita aikinsu ga abin da ya kawo su Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina kira a gare ku da ku bi dokokin jakadanci domin ganin cewa kun tsaya a layin aikinku a yayin da ku ke sa ido a kan shirin zabe da shi kan shi zaben.
Ina ma iyi maku fatan nasara a wajen aikinku tare da karfafa maku gwiwa da ku yi amfani da damar ku domin jin dadin irin arzikin da ke kasar nan."

- Muhammadu Buhari

Buhari
Sababbin Jakadu a Aso Rock Hoto: @femi.adesina.1023
Asali: Facebook

Matsalolin da ke damun Afrika ta Yamma

Wani rahoto daga Tribune ya nuna shugaba Buhari ya shaidawa sababbin Jakadun da aka aiko zuwa Najeriya ana kokarin magance rashin tsaron Afrika.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Bayyana Ainihin Manufar Ƙirƙirar Ƙungiyar Boko Haram

Baya ga haka, Buhari ya ce Najeriya ta na aiki da kungiyar ECOWAS wajen ganin yadda za su yaki kifar da gwamnati da ake yi a wasu kasasen Nahiyar.

A cewar shugaban na Najeriya, matsalolin garkuwa da mutane, satar dabbobi, ta’adanci, da safarar mutane da kwayoyi sun fi karfin gwamnatin kasa.

A jawabinsa, ya yi kira ga kasashen Switzerland, Suwidin, Ireland, Thailand, Sanagal da Sudan su bada gudumuwa a magance matsalolin yammacin Afrika.

Sababbin jakadun da suka zo Najeriya su ne; Nicolas Lang, Annika Hahn Englund, Peter Ryan, Kitiisak Klomchit, Nicolas Nyouky, sai kuma David Chaot.

Magana ta kare a kan batun zabe

Rahoton da muka fitar a baya, ya nuna cewa Mai girma Shugaban Najeriya ya tabbatar da zaben 2023 yana nan a ranar da Hukumar INEC ta tsaida

Muhammadu Buhari ya shaida haka a lokacin da Rabaren Lucius Iwejuru Ugorji ya jagoranci wasu Fastoci zuwa wajensa a kan batun zaben a Aso Villa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Buhari Ya Bayyana Wani Muhimmin Dalili 1 Da Zai Sa Arewa Ta Zabi Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel