PDP Ta Dauko Sabon Salo, Tana Kokarin Hada-Kai da Jam’iyyu 11 Domin Kifar da APC

PDP Ta Dauko Sabon Salo, Tana Kokarin Hada-Kai da Jam’iyyu 11 Domin Kifar da APC

  • Babbar jam’iyyar hamayyar Najeriya watau PDP, za tayi koyi da APC wajen hada karfi da karfe a 2023
  • Sakataren yada labaran PDP a Najeriya ya tabbatarwa Duniya su na kokarin hada-kai da jam’iyyu 11
  • Ibrahim Abdullahi ya ce jam’iyyun siyasar da ba su da karfi za su goyi bayan takarar Atiku Abubakar

Abuja - Ganin zabe ya karaso gadan-gadan, jam’iyyar PDP mai adawa ta shiga tattaunawa da wasu kananan jam’iyyu domin su ba su hadin-kai.

Babbar jam’iyyar hamayyar ta tabbatarwa Punch haka a ranar Laraba, 11 ga Junairu 2023.

Wannan yana zuwa ne jim kadan bayan rahotanni sun zo cewa Bola Tinubu da jam’iyyar APC sun bazama neman goyon bayan wasu jam’iyyu.

Da aka tattauna da Sakataren yada labaran PDP na kasa, Ibrahim Abdullahi, ya tabbatar da cewa sun fara zama ‘yan kananan jam’iyyun kasar.

Kara karanta wannan

Rigingimun PDP: Daga Karshen Atiku Ya Sake Rokon Gwamnanonin G5

Ibrahim Abdullahi yake cewa jam’iyyarsu ta PDP ta na magana da jam’iyyu kusan 12, kuma a shirye take ta zauna da wasu kungiyoyin a kan takara.

Legit.ng Hausa ba ta da labarin sunayen jam’iyyun nan da ake cewa ana neman su hada-kai da PDP da kuma ‘dan takaranta, Alhaji Atiku Abubakar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jam'iyyar
Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Jam'iyyu 11 za su bi PDP?

“Akwai su da-dama, amma rashin dabara ne in fito fili in ambace su. A lokacin da na bincika a karshe, mu na magana da fiye da 11 a cikinsu.
Sun dumfare mu da niyyarsu na yin aiki tare da mu wajen tabbatar da an yi zaben gaskiya a 2023.
Abin da suka fada mana kenan, amma ni da kai duk mun san abin da wannan maganar take nufi.
Jam’iyyu ne da ‘yan takaransu ba su da karfi sosai. Ina tabbatar maku da cewa akwai tsarin da yake kasa, kuma muna son ganin ire-irensu.

Kara karanta wannan

Ma’aikatan Najeriya Sun Ayyana Wadanda Za Su Zaba Daga Sama Har Kasa a 2023

Idan mu ka hada-kai tare, za mu ceci kasar nan. Sun san karfin PDP da kuma tarihin ‘dan takaranmu na shugaban kasa, Atiku Abubakar.

- Ibrahim Abdullahi

APC ta samu baraka a Enugu

An ji rahoto cewa wadanda ake ji da su a APC a Enugu ba su je wajen yi wa Bola Tinubu kamfe ba, sun bayyana dalilinsu na fushi da Jam’iyyar.

Bisa dukkan alamu rikicin gidan jam’iyyar APC ya yi tasiri yayin da Bola Tinubu ya je yawon kamfe a Jihar Enugu, kuma zai iya yin tasiri wajen zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel