Abin da Ya Faru Shekaru 30 da Suka Wuce, Zai Sake Faruwa a Zaben 2023 – Ganduje

Abin da Ya Faru Shekaru 30 da Suka Wuce, Zai Sake Faruwa a Zaben 2023 – Ganduje

  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya dage wajen tallata takarar Bola Tinubu na APC a jihar Kano
  • Dr. Abdullahi Ganduje yake cewa yadda aka zabi MKO Abiola a 1993, haka za a goyi bayan Tinubu a 2023
  • Tun da mulki yana Arewa tun 2015, Gwamnan na Kano yana ganin ya kamata yanzu ya koma Kudu

Kano – A wajen Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, abin da ya wakana a lokacin zaben 1993, zai sake maimaita kan shi a zaben bana.

Yayin da ‘yan makonni suka rage a gudanar da zaben sabon shugaban kasa, Vanguard ta rahoto Abdullahi Umar Ganduje yana hango nasara.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana ne a wajen yakin neman zaben jam’iyyar APC da suka ziyarci Hakimin Kibiya, Alhaji Sunusi Abubakar Ila.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Zama da ‘Yan Kwamitinsa, APC Ta Fara Shiga Kawance da Wasu Jam'iyyu

Gwamnan da ‘yan tawagar yakin neman zaben APC a Kano sun yi zama da mutane a Rano da Bunkure, sannan suka kwana a masarautar kasar Rano.

Kanawa za su zabi APC - Ganduje

Babban sakataren yada labaran Gwamnan Kano, Abba Anwar ya rahoto Dr. Ganduje yana cewa mutanen jihar Kano za su marawa APC baya a zabe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Kwarewa a kan siyasa da dattakunan mutanen Kano ya jawo suka zabi Cif MKO Abiola na SDP kuma suka yi watsi da Bashir Othman Tofa na NRC."

- Abdullahi Umar Ganduje

Ganduje
Gwamna Ganduje wajen yakin zaben APC a Kano Hoto: @aaibrhim1
Asali: Facebook

Jawabin yake cewa wannan ya nuna jihar Kano ta yarda da hadin-kan kasa da kuma cancanta. Jaridar Daily Post ta fitar da labarin nan a ranar Laraba.

Tinubu ya marawa Arewa baya a baya

Gwamna Ganduje ya tunawa mutanen Najeriya Bola Ahmed Tinubu mai neman zama shugaban Najeriya a APC ya rika goyon bayan ‘Yan Arewa.

Kara karanta wannan

Kujerarsu ta na rawa: Gwamnonin Jihohi 4 da Sai Sun Yi da Daske Za Su Koma Mulki

“Tinubu ya yi ruwa da tsaki wajen zaman Atiku Abubakar ‘dan takaran shugaban kasa a AC. Kuma shi ne ya ba Nuhu Ribadu damar takara a ACN."

- - Abdullahi Umar Ganduje

An rahoto Ganduje yana cewa abin da ya kamata shi ne mulki ya rika yawo tsakanin Kudu zuwa Arewa, yake cewa yanzu lokaci ne da ‘Yan Kudu za su dana.

A ra’ayin Ganduje mai shirin barin ofis, Asiwaju Tinubu ya fi duk masu neman zama shugaban kasa cancanta, ya ce a zabe shi da sauran ‘yan takaran APC.

Rikicin APC ya bayyana a Enugu

An ji labari duk wadanda ake ji da su a tafiyar APC a jihar Enugu ba su je wajen yi wa Bola Tinubu kamfe ba, sun bayyana dalilinsu na fushi da Jam’iyyar.

Bisa dukkan alamu rikicin gidan jam’iyyar APC ya yi tasiri yayin da tawagar Tinubu ta je yawon kamfe a Jihar Kudu maso gabashin kasar a makon nan.

Kara karanta wannan

An Tono Babban Abinda APC Ta Rasa a Arewa Wanda Zai Ja Wa Tinubu Shan Kaye a Zaben 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel