Mutum 2 Za Su Taimaki APC ta Koma kan Mulki Inji ‘Dan Majalisar da ya bar NNPP

Mutum 2 Za Su Taimaki APC ta Koma kan Mulki Inji ‘Dan Majalisar da ya bar NNPP

  • Hon. Shamsudeen Danbazzau ya fi ganin nasarar Jam’iyyar APC a kan PDP, LP ko NNPP a 2023
  • ‘Dan majalisar wakilan tarayyar ya ce Rabiu Kwankwaso da Peter Obi za su share masu hanya
  • Danbazzau yake cewa a lokacin da PDP, LP da NNPP take wawaso, Bola Tinubu zai tattara kuri’u

Abuja - Shamsudeen Danbazzau yana ganin samun wani fitaccen ‘dan siyasa yana takara a zaben 2023, shi zai taimakawa Bola Ahmed Tinubu lashe zabe.

A rahoton Premium Times na ranar Alhamis, 12 ga watan Junairu 2023, Hon. Shamsudeen Danbazzau ya yi bayanin yadda jam’iyyar APC za tayi nasara.

Shamsudeen Danbazzau mai wakiltar Takai da Sumaila a karkashin APC a majalisar tarayya ya ce Rabiu Kwankwaso da Peter za su taimakawa jam’iyyarsu.

‘Dan siyasar yana ganin ‘yan takaran na LP da NNPP za su bata ruwa, kuma ba za su sha ba, a karshen hakan zai yi sanadiyyar da Bola Tinubu zai ci zabe.

Kara karanta wannan

Takarar 2023: Yadda Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi Za Suyi Yaki a Kan Kuri’un Kano

Kuri'un PDP za su rabu 2 a 2023

A cewar ‘dan majalisar, Kwankwaso da Obi za su raba kuri’un Atiku Abubakar da PDP zuwa biyu. Ana ganin Atiku ne babban barazanar da APC take fuskanta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kafin su shiga takarar kujerar shugabancin Najeriya a LP da NNPP, Obi da Sanata Kwankwaso duk ‘yan jam’iyyar PDP ne da suka taimakawa Atiku a 2019.

APC a Kano
Yakin neman zaben APC a Kano Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Punch ta ce Shamsudeen Danbazzau ya bayyana wannan da ya yi hira da ‘yan jarida a majalisa, a nan ya nuna Tinubu yana da lafiyar da zai jagoranci jama’a.

Atiku zai yi rashin Obi da Kwankwaso

Obi ya yi tasiri wajen kuri’un da Atiku Abubakar ya samu a Kudu maso gabas da Kudu maso kudu, da alama wannan karo 'yan yankin za su karkata ga LP.

Kwankwaso yana da mabiya a jihar Kano da ya fito da wasu yankunan Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Kakakin PDP Ya Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar Kwankwaso a Jihar Arewa

A cewarsa, yayin da jam’iyyun PDP, LP da NNPP suke yaki wajen samun kuri’unsu a yanki daya, salin-alin Asiwaju Tinubu da Shettima za su samu galaba.

Siyasar Kano

Irina bin da zai faru kenan a zaben Gwamnan jihar Kano, Danbazau ya ce Sha’ban Sharada na ADC zai saukakawa Nasiru Gawuna wajen doke Abba Yusuf.

Jaridar ta rahoto ‘dan majalisar tarayyar wanda ya yi zama na ‘yan kwanaki a NNPP yana cewa tasirin Kwankwasiyya ba zai hana APC lashe zabe a Kano ba.

Kuri'u 5.9 su na jihar Kano

An ji labari Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi sun kwallafa rai a kan kuri’un da za su fito daga Jihar Kano a zabe mai zuwa.

‘Yan Takaran kujerar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyun APC, PDP, NNPP da LP sun fito da dabarun da za su cece su a jihar mai kuri’u kusan miliyan shida.

Kara karanta wannan

PDP Ta Dauko Sabon Salo, Tana Kokarin Hada-Kai da Jam’iyyu 11 Domin Kifar da APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel