INEC Ta Tsawaita Lokacin Dena Bada Katin Zabe Na PVC Gabanin Zaben 2023

INEC Ta Tsawaita Lokacin Dena Bada Katin Zabe Na PVC Gabanin Zaben 2023

  • Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta amince za ta tsawaita wa'adin karbar katin zabe na PVC a sassan kasar bayan korafi daga yan Najeriya
  • Za a iya yin karin da kwanaki 7 zuwa 8 bisa yanayin yadda ake karbar katin a jihohin kasar
  • INEC din kuma ta sha alwashin daukan matakin hukunta duk wani jami'inta da ake zargi da nuna banbanci wurin rabon katin

FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta na kasa, INEC, ta sha alwashin tsawaita kwanakin cigaba da karbar katin zabe na dindindin wato, PVC zuwa ranar Lahadi, 29 ga watan Janairu.

A baya, hukumar ta sanar da ranar Lahadi, 22 ga watan Janairu a matsayin ranar dakatar da karbar katin na PVC.

Hukumar INEC
INEC Ta Tsawaita Lokacin Dena Bada Katin Zabe Na PVC Gabanin Zaben 2023. Hoto: Hukumar INEC
Asali: Facebook

Sai dai an yanke shawarar tsawaita bada katin ne bayan wani taro da aka yi a ranar Alhamis, 12 ga watan Janairu da manyan jami'an hukumar suka yi.

Kara karanta wannan

Jami'an Tsaron Nigeria Sun Sanar Da Halaka Yan Ta'adda Kusan 50, Kuma Sun Kama 62

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwamishinan INEC, Festus Okoye ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da Legit.ng ta gani.

"Hukumar tana son dukkan masu zabe da suka yi rajista su samu damar karbar PVC dinsu gabanin zaben. Don haka, an tsawaita ranar dena bada katin da kwana takwas.
"A maimakon ranar Lahadi 22 ga watan Janairun 2023, za a cigaba da bada PVC har zuwa ranar 29 ga watan Janairun 2023. A halin yanzu, lokacin karbar shine daga karfe 9 na safe zuwa 3 na rana a kullum. (har da Asabar da Lahadi)."

Ga bayani game da karin wa'adin da aka yi kamar haka:

1. An tsawaita karbar kati daga gunduma da sati daya wato daga ranar Litinin 16 ga watan Janairu zuwa Lahadi 22 ga watan Janairun 2023

2. Za a cigaba da karbar kati daga karamar hukuma daga ranar Litinin 23 zuwa Lahadi 29 ga watan Janairun 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hukumar Zabe INEC Ta Kara Wa'adin Karban Katin PVC Da Kwanaki 8

A cewar kakakin na INEC, bayan samun cewa wasu jami'an hukumar na take hakkin yan Najeriya wurin karbar katin, za ta fara sa ido da bincike kan zargin.

Ya kara da cewa:

"Duk wadanda aka samu da laifi za su fuskanci hukunci/shari'a
"Hakazalika, hukumar ta damu bisa rahoton zargin nuna banbanci da ake yi a wurin bada katin na PVC a wasu yankuna. Hakan ya saba wa doka. Dukkan wadanda suka yi rajista bisa ka'ida suna da ikon karbar katinsu don su yi amfani da shi su yi zabe a duk sassan kasar nan inda suka yi rajista."

Hukumar INEC ta bayyana adadin yan Najeriya da suka yi rajista a zaben 2023

A bangare guda, hukumar zaben Najeriya, INEC, ta sanar da cewa mutane kimanin 93,469,008 ne suka yi rajista don zaben 2023.

Alkallumar sun nuna cewa kashi 52.5 cikin 100 cikin masu rajistan maza ne yayin da kashi 47.5 cikin 100 kuma mata ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel