Kar Yan Nigeria Su Damu Za'ai Zabe Ba Abinda Zai Hana Ai Zabe A Kasar Nan

Kar Yan Nigeria Su Damu Za'ai Zabe Ba Abinda Zai Hana Ai Zabe A Kasar Nan

  • Kwana arba'in da biyar ya rage a kada kuri'a a Nigeria dan zabar sabon shugaban kasar Nigeria da zai mulki kasar tsawon shekara hudu
  • Ba sabon abu bane a Nigeria batun daga ranar gudanar da zabe, domin ya faru a shekarar 2015 da kuma shekarar 2019
  • Har yanzu ma dai wasu kungiyoyi da dai-daiku na ganin za'a dage zaben, domin hukumar zaben bata shirya ba

Abuja - Gwamnatin tarayya Nigeria ta tabbatar da yan Nigeria za'a gudanar da zabe a watan gobe mai kamawa, rahotan jaridar Vanguard

Ministan labarai da al'adu Mr Lai Muhammad ne ya bada tabbacin a wani gabatar da muhimman abubuwan da shugaba Buhari ya cimma daga 2015 zuwa 2023.

Ministan na wannan batun ne bayan da hukumar zaben Nigeria tace za'a iya daga zabe ko kuma soke shi ma indai matsal-tsalun tsaro na kara ta'azzara a kasar.

Kara karanta wannan

Bayar Da Ilimi Mai Nagarta Shine Zai Kawo Karshen Boko Haram A Nigeria Inji Buhari

Zaben
Kar Yan Nigeria Su Damu Za'ai Zabe Ba Abinda Zai Hana Ai Zabe A Kasar Nan Hoto: UCG
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban hukumar zaben Nigeria, Farfesa Mahmoud Yakubu wanda ya samu wakilcin Shugaban cibiyar horar da ma'aikata na INEC, Prof Abdullahi Abdu Zuru,yace:

"In dai Nigeria bata sa ido ba, kuma bata ci gaba da daukan kwararan mataki ba wajen wannan matsaltsalun tsaron nan ba, tu akwai yiwuwar dage ko soke zabe a kasar nan"

Ba Maganar Dage Zabe

Ministan yace tabbas za'ai zabe, kuma gwamnatin tarayya tana sane da yadda hukumar zabe ke hada hannu da gwuiwa da hukumomin tsaro dan ganin an magance tare da nyin zabe cin aminci

Lai Muhammad ya ci gaba da cewa:

"Bari nai amfani da wannn damar nai martani ga wanda suke soki-burutsu a kafafen yada labarai kan cewa baza ai zabe ba sabida wasu matsaloli"
"To ina mai tabbatar muku gwamnatin tarayya ta tsaya tsayin daka dan ganin zaben 2023 ya gudana kamar yadda aka tsara shi ba gudu-ba-ja da bayaa duk fadin Nigeria

Kara karanta wannan

2023: Tinubu, Kwankwaso da Obi za su tashi a tutar babu, malami ya hango magajin Buhari

Lai muhammad yace muna tabbatar da yan kasar nan su kwantar da hankalinsu, kuma su kasance cikin shirin jefa kuri'a a yan kanakin da suka rage dan jefata.

Abin jira a gani nan shine ko tarihi zai maimata kansa kamar yadda aka gani a zabukan baya da suke shude ko kuma za'a gudanar da zaben kamar yadda aka shirya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel