Shin Peter Obi Ya Talauce Ne? Bayanai Sun Fito Yayinda Gwamnatin UK Ta Rushe Kamfanin Dan Takarar Jam'iyyar LP

Shin Peter Obi Ya Talauce Ne? Bayanai Sun Fito Yayinda Gwamnatin UK Ta Rushe Kamfanin Dan Takarar Jam'iyyar LP

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour a halin yanzu yana fama da kallubale
  • Gwamnatin Birtaniya ta rushe kamfanin Next International (UK) Limited mallakar tsohon gwamnan Anambra
  • An tattaro cewa kamfanin ta gaza mika bayanai game da hada-hadar kudadenta na shekara cikin wa'adi bayan an bada gargadi

Gwamnatin Birtaniya ta soke ayyukan kamfanin Next International (UK) Limited mallakar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi.

Kamar yadda Premium Times ta rahoto, an 'rushe' Next International (UK) Limited ne saboda gazawarta na gabatar da bayanan hada-hadar kudinta na shekara-shekara.

An rahoto cewa an soke kamfanin ne tun Satumban 2021 bayan an tabbatar da cewa an bada gargadin farko da na biyu na cewa za a 'soke' ta.

Mr Peter Obi
Shin Peter Obi Ya Talauci Ne? Bayanai Sun Fito Yayinda Gwamnatin UK Ta Rushe Kamfanin Dan Takarar Jam'iyyar Labour. Hoto: Peter Obi
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro gwamnatin Birtaniya ta amince da ka'idar na 'soke' kamfani idan ta gaza gabatar da takardar hada-hadar kudinta ko ta gaza sanar da gwamnati idan ta canja adireshinta na kasuwanci.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar PDP Ta Fusata, Ta Kori Dan Takarar Gwamna a Jihar Arewa Kan Abu 3

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sauran bayanai sun nuna cewa idan aka hukunta kamfani wanda ya gaza cika ka'idoji, za a cire bayanansa daga rajistan sunayen kamfanoni, hakan na nufin ba ya aiki kenan.

An bawa NEXT wasikar sanarwa

Kazalika, kafin a cire bayanan kamfani daga kafar da al'umma ke hada-hada, gwamnatin Birtaniya ta wajbatawa magatakardar Companies House ya tura a kalla wasikar gargadi biyu ga kamfanin da abin ya shafa. Wannan zai iya zama hujja na 'soke' kamfanin nan take.

A batun Next International, an tattataro cewa ba ta amsa wasikun gargadin da aka tura mata daga 22 ga watan Yunin 2021 (na farko) da 31 na Agustan 2021 (na biyu) hakan ya yi sanadin rushe kamfanin baki daya a ranar 7 ga watan Satumban 2021.

Bayanai sun nuna cewa har sau hudu (2017, 2018, 2019 da 2020) an bawa Next International wasikar gargadi kan rashin mika bayanan hada-hadar kudinta a kan lokaci.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: IGP ya Samu Takardar Umarnin Kamo ‘Dan Takarar Gwamnan Akwa Ibom Kan Zargin Damfara

Takalman da Peter ya saka a wurin kamfen a Jihar Imo ya janyo cece-kuce

A wani rahoton, Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour ya nuna rashin girman kansa har a wurin kamfen dinsa.

Tufafin da Obi ya saka a taron kamfen dinsa na Owerri, babban birnin Imo a ranar 6 ga watan Disamban ya janyo hankalin wasu yan Najeriya a kafafen sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel