Kwankwaso Ya Sha Alwashin Mai da Wa’adin Sakamakon JAMB Ya Koma Tsawon Shekaru 4

Kwankwaso Ya Sha Alwashin Mai da Wa’adin Sakamakon JAMB Ya Koma Tsawon Shekaru 4

  • Dan takarar shugaban kasa a NNPP ya ci alwashin kawo sauyi a fannin ilimi a Najeriya idan aka zabe shi
  • Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya ce zai sa JAMB, WAEC da NECO da sauransu duk su zama kyauta
  • Ya kuma ce, zai mai da wa'adin lalacewar jarrabawar JAMB ya koma shekaru hudu saboda wasu dalibai

Jihar Bauchi - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNNP, Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya yi alkawarin mai da wa'adin jarrabawar UTME ta JAMB ta zama shekaru hudu idan ya gaji Buhari.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da tutar jam'iyyar NNPP ga 'yan takarar gwamna a jihohin Arewa maso Gabas shida da kuma na sanata 18 a ranar Alhamis a jihar Bauchi.

Ya bayyana cewa, akwai dalibai da yawa da ke samun sakamako mai kyau na JAMB, amma ba sa samun damar samun gurbin karatu a shekarar sabida wasu dalilai, rahoton PM News.

Kara karanta wannan

eNaira: 'Yan zamani sun more, an kawo wata hanyar biyan rajistar JAMB cikin sauki

Kwankwaso ya je Bauhci, ya yi magana game da JAMB
Kwankwaso Ya Sha Alwashin Mai da Wa’adin Sakamakon JAMB Ya Koma Tsawon Shekaru 4 | Hoto: @KwankwasoRM
Asali: UGC

Dalibai suna kokari, amma babu gurbin shiga jami'a

Ya ce idan haka ta faru ba laifinsu bane, don haka gwamnati za ta zo da hanyar share musu hawaye kowa ma ya huta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Ana kakabawa wadannan daliban da iyayensu kudi domin sake rubuta jarrabawa a duk shekara amma idan aka zabe mu za su mai da wa'adin JAMB ya zama shekaru hudu."
"Za mu ba da wa'adin shekaru hudu ga JAMB domin 'ya'yanmu su yi amfani da sakamakon jarrabawar su samu gurbin karatu a manyan makarantu a wannan lokacin."

Dan takarar ya kuma yi alkawarin bayar da fom din neman gurbin shiga jami'a da kuma na neman aiki kyauta ba da kudi ba.

A cewarsa:

"Za mu inganta tare da fadada jami'o'inmu, kwalejin fasaha da kuma kwalejin ilimi kuma mu habaka ingancinsu su yi gogagga da duniya.

Kara karanta wannan

2023: Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Karar da NNPP Ta Shigar da Dan Takarar APC

"Gwamnatina za ta gina ajujuwa 500,000 a fadin kasar, domin daukar yaran da ba sa zuwa makaranta sama da miliyan 20 a saka su a makaranta.
"Za mu sanya dukkan jarrabawar WASC, NECO, NABTEB, NBAIS, JAMB da sauransu duk su zama kyauta."

Su waye 'yan takarar NNPP a jihohin Arewa maso Gabas?

Kwankwaso ya ce dukkan 'yan takarar gwamnan NNPP a Arewa maso Gabas sun cancanta,, kuma za su iya samar da mulki na gari ga al'ummar jihohinsu.

'Yan takarar NNPP na gwamna a yankin sun hada da Sa'adu Tahir na jihar Adamawa, Sanata Haliru Jika na jihar Bauchi, da Dr Umar Alkali na jihar Borno.

Hakazalika, akwai Muhammad Mailantarki na jihar Gombe, Yahaya Sani a jihar Taraba da kuma Umar Alhaii a jihar Yobe, People Gazette ta tattaro.

Da yake magana, dan takarar gwamnan jihar Bauchi, Sanata Jika ya bukaci magoya bayansa da su kasance masu amana da jajircewa, kuma su ba NNPP sama har kasa dodar dukkan kuri'unsu.

Kara karanta wannan

A Gaban Buhari a Yobe, Bola Tinubu Ya Faɗi Matakin da Zai Dauka Kan ASUU Idan Ya Ci Zaben 2023

Kwankwaso ya bayyana a baya cewa, ya karar da kudadensa da kadarorinsa da yawa don daukar nauyin karatun matasa a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.