Jihar Edo
Phillip Shaibu, mataimakin gwamnan Edo, ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP na zaben gwamnan jihar na 2024, yayin da ake jiran tsagin Gwamna ya yi nasa.
Bayan shafe sa'o'i a ofishin ‘yan sanda, rundunar ta sanar da sakin shugaban jam’iyyar LP ta kasa, Julius Abure da aka cafke a jiya Laraba 21 ga watan Faburairu.
Rahotanni sun nuna cewa dakarun ƴan sanda sun kama Barista Julius Abure, shugaban jam'iyyar Labour Party (LP) na ƙasa a Benin City, babban birnin Edo.
Rikicin cikin gidan APC ya birikice har ta kai an kira taro na gaggawa. Abdullahi Umar Ganduje ya yi zaman gaggawa da shugabanni bayan samun ‘yan takara 3 a zabe 1
Jam’iyyar APC a Najeriya ta ayyana zaben fidda gwanin jihar Edo wanda bai kammala ba bayan bayyanar 'yan takarar jam'iyyar har guda uku bayan kammala zaben.
Anamero Dekeri, daya daga cikin ‘yan takara uku a zaben fidda gwanin gwamna na APC a jihar Edo, ya dira sakatariyar jam’iyyar na kasa a ranar Litinin.
Sa'o'i 48 bayan zaben fidda gwani, matasan jam'iyyar APC sun ɓalle da zanga-zangar adawa da ayyukan SWC ta jihar Edo, sun buƙaci masu ruwa da tsaki su rushe ta.
Tsohon kwamishina a jihar Edo, Andrew Emwanta, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC biyo bayan zaben fidda gwani na gwamna na jam'iyyar da aka gudanar.
An rasa gane wanene halataccen 'dan takaran APC a zaben Gwamnan Edo domin kuwa an ba Hon. Dennis Idahosa, Sanata Monday Okpebholo da Anamero Sunday Dekeri tikiti.
Jihar Edo
Samu kari