Edo 2024: Kwankwaso Ya Magantu Kan Nasarar Malamin Addini a Matsayin Dan Takarar Jam’iyyar NNPP

Edo 2024: Kwankwaso Ya Magantu Kan Nasarar Malamin Addini a Matsayin Dan Takarar Jam’iyyar NNPP

  • Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar Edo, Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi martani bayan zaben fidda gwanin NNPP
  • Kwankwaso ya ce tabbas jam’iyyarsu ta fitar da dan takara wanda ya ke da matukar kyau a zaben da za a gudanar
  • Sanatan ya bayyana haka ne a shafinsa na X a daren jiya Litinin 26 ga watan Faburairu bayan tarbar kwamitin a gidansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya taya kwamitin zaben fidda gwanin jihar Edo murnar kammala zaben lafiya.

Sanatan ya ce nasarar Fasto Azemhe Azena abin murna ne ganin yadda jam’iyyar NNPP ta fitar da dan takara da ya dace.

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin addini ya yi nasarar zama dan takarar gwamna a jam'iyyar NNPP, bayanai sun fito

Kwankwaso ya yi tsokaci kan takarar NNPP a zaben jihar Edo
Kwankwaso ya taya Azena murnar nasarar lashe zaben fidda gwani. Hoto: Dr. Azehme Azena, Rabiu Kwankwaso.
Asali: Facebook

Menene Kwankwaso ke cewa kan zaben Edo?

Kwankwaso ya bayyana haka ne a shafinsa na X a daren jiya Litinin 26 ga watan Faburairu bayan tarbar kwamitin zaben a gidansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan jigon jam’iyyar ya karbi bakwancin Sanata Kawu Sumaila wanda shi ne ke jagorantar kwamitin zaben a jihar.

A cewarsa:

“Na yi murna da karbar Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila wanda ke jagorantar zaben fidda gwanin jihar Edo da sauran mambobin kwamitin a gida na a yau.
“Na taya su murnar samun nasarar kammala wannan aiki inda Dakta Azemhe Azena ya yi nasara a zaben da aka gudanar.
“Yayin da muke shirye-shiryen tunkarar zabe, ina da tabbacin cewa jam’iyyarmu ta tsayar da dan takara mafi kyau ga al’ummar jihar Edo.”

Azena ya yi nasara a zaben fidda gwani

Wannan na zuwa ne bayan jam’iyyar ta kammala gudanar da zaben fidda gwanin yayin da ake shirin gudanar da zaben a watan Satumbar wannan shekara.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Ganduje ya fadi babban dalilin da zai sa su yi wa PDP dukan alatsine a zabe, ya bugi kirji

Fasto Dakta Azemhe Azena shi ne ya yi nasarar kasancewa dan takarar jam’iyyar wanda hakan ya saka al’ummar jihar murna saboda tasirinsa.

Hakan ya biyo bayan kammala zabubbukan fidda gwanin da sauran jam’iyyun APC da PDP da LP suka gudanar.

An bai wa Kwankwaso shawara a siyasa

Kun ji cewa wani lauya mazaunin kano ya bai wa Sanata Rabiu Kwankaso shawarar gina siyasarsa a Najeriya.

Lauyan mai suna Umar Sa’ad Hassan ya ce Kwankwaso ya na da matukar tasiri da mutunci a siyasar jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel