Mataimakin Gwamna Ya Kara Haddasa Sabuwar Rigima a Jam'iyyar PDP Kan Takarar Gwamna

Mataimakin Gwamna Ya Kara Haddasa Sabuwar Rigima a Jam'iyyar PDP Kan Takarar Gwamna

  • Rigingimun da suka dabaibaye jam'iyyar PDP a jihar Edo ƙarƙashin Gwamna Godwin Obaseki sun ɗauki sabon salo bayan zaɓen fidda gwani
  • Mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu, ya jaddada cewa shi ne halastaccen ɗan takarar PDP a zaben gwamna mai zuwa a watan Satumba, 2024
  • Asue Ighodalo ne ya lashe zaɓen fidda gwani bayan doke manyan ƴan takara 9 ciiki harda Shaibu a zaɓukan da aka yi a wurare daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya ce shi ne halastaccen ɗan takarar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jihar da ke tafe.

Shaibu ya bayyana haka ne ranar Jumu'a, 23 ga watan Fabrairu, 2024 yayin da ya baƙunci shirin Sunrise Daily na gidan talabijin ɗin Channels.

Mataimakin gwamna ya kara tada rikici a PDP.
Sabon Rikici Ya Barke a Jam'iyyar PDP Kan Tikitin Takarar Gwamnan Jihar Edo a Zaben 2024 Hoto: Philip Shaibu, Godwin Obaseki
Asali: Facebook

Waye ya ci zaɓen fidda gwanin PDP a Edo?

Kara karanta wannan

Edo: Bayan matsalar da aka samu, APC ta bayyana wanda ya lashe tikitin takarar gwamna

Idan baku manta ba, Shaibu ya lashe zaben fidda gwani na tsagi ɗaya ranar Alhamis yayin da tsohon shugaban bankin Sterling, Asue Ighodalo ya samu nasara a tsagi ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi bayan samun nasara, mataimakin gwamnan ya ce zaɓen da Ighodalo ya lashe bai bi tsarin doka da ƙa'idojin jam'iyyar PDP ba.

Mista Shaibu ya ce:

"Idan da sun bi dukkan matakai da ƙa'idojin mu a filin kwallo za a yi zaɓen kuma idan na yi nasara shikenan, idan na sha kaye zan taya wanda ya samu nasara murna kuma na mara masa baya.
"Mu tara mun amince a bi matakan da ya dace kuma mun yarda zamu yi aiki da duk wanda ya samu nasara.
"Ba zai yiwu mutun tara su haɗu kan abu ɗaya, mutum ɗaya ya banɗare amma a ɗauki maganar ɗaya a bar sauran 9, hankali ba zai ɗauka ba."

Kara karanta wannan

Edo: Murna yayin da deleget ta haihu a wurin zabe, ta raɗa wa jaririn suna mai ban mamaki

Shin mataimakin gwamnan ya tuntuɓi Ighodalo?

Shaibu ya ƙara da cewa ya tuntubi Ighodalo domin ya zo su haɗa kai su yi aiki tare domin nasarar PDP.

"Tuni na tura masa saƙo domin ya zo mu yi aiki tare saboda nine halastaccen ɗan takara, wanda nan gaba kowa zai gane haka. Zan yi duk yadda zan yi na haɗa kan mu."

Wanene ɗan takarar APC a jihar Edo?

A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC ta ayyana Sanatan Edo ta Tsakiya, Monday Okpebholo, a matsayin ɗan takararta a zaben gwamnan jihar Edo mai zuwa a 2024.

Shugaban kwamitin zaben fidda gwani, Gwamna Bassey Otu, ya bayyana Okpebholo a matsayin wanda ya samu nasara da ƙuri'u 12,433.

Asali: Legit.ng

Online view pixel