Edo 2024: Ganduje Ya Fadi Babban Dalilin da Zai Sa Su Yi Wa PDP Dukan Alatsine a Zabe, Ya Bugi Kirji

Edo 2024: Ganduje Ya Fadi Babban Dalilin da Zai Sa Su Yi Wa PDP Dukan Alatsine a Zabe, Ya Bugi Kirji

  • Yayin da ake shirye-shiryen zaben gwamnan jihar Edo, Abdullahi Ganduje ya sha alwashin kan samun nasara a zaben
  • Shugaban jam’iyyar ya ce APC ta na da tabbacin samun nasara saboda dan takarar da ta tsayar mai kyau ne kuma zabin al’umma
  • Shugaban jam’iyyar ya bayyana haka ne a yau Asabar 24 ga watan Faburairu yayin ba da satifiket ga Okpebholo bayan ya yi nasara

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya na da tabbacin jam’iyyar za ta yi nasara a zaben jihar Edo.

Ganduje ya ce komai ya nuna alamu jam’iyyar ce za ta lashe zaben bayan zaban Sanata Monday Okpebholo, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Kwanaki 3 bayan nasarar Kwankwaso a kotu, uban NNPP ya nemi hadin kai kan abu 1 game da Tinubu

Ganduje ya bugi kirji kan irin shirin da suka yi wa zaben Edo
Ganduje ya sha alwashin lashe zaben Edo da mummunan kaye. Hoto: Umar Ganduje.
Asali: Facebook

Menene Ganduje ke cewa kan zaben Edo?

Shugaban jam’iyyar ya bayyana haka ne a yau Asabar 24 ga watan Faburairu yayin ba da satifiket ga Okpebholo bayan ya yi nasara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an gudadar da zaben fidda gwanin ne a unguwanni 192 a jihar inda ya ce daga bisani Okpebholo ya yi nasara.

A cewarsa:

“Abin da kawai muke bukata shi ne hadin kai a tsakanin ‘yan takarar don yin nasara bayan zaben fidda gwanin."

Babban dalili Ganduje na cin zaben

Ya kara da cewa:

“Jam’iyyar mu ta na da dan takara mai kyau wanda aka shirya shi kuma jama’a za su zabe shi don Okpebholo kuma ya shirya cin zaben.”

Ganduje ya kara da cewa sauran ‘yan takarar da ba su yi nasara ba tuni suka taya Okpebholo murnar lashe zaben, cewar The Eagle.

Kara karanta wannan

Obaseki Vs Shaibu: Mataimakin gwamnan Edo ya lashe zaben fidda gwani na kujerar gwamna a PDP

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar a ranar 21 ga watan Satumbar wannan shekara.

Ganduje ya rasa jiga-jigai

Kun ji cewa shugaban jam’iyyar APC a Najeriya, Dakta Umar Ganduje ya tafka babban asara a jihar Kano.

Akalla ciyamomin kananan hukumomi uku ne suka watsar da kashin jam’iyyar tare da sauya sheka zuwa NNPP a jihar.

Yayin da ya ke karbar sabbin tuban, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya ce ya ji dadi da suka yi tunanin inda ya ce sun zama daya da sauran ‘yan jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel