Mataimakin Gwamnan Ya Kara Tada Rigima, Ya Dira Sakateriyar PDP Ta Ƙasa Kan Muhimmin Abu 1

Mataimakin Gwamnan Ya Kara Tada Rigima, Ya Dira Sakateriyar PDP Ta Ƙasa Kan Muhimmin Abu 1

  • Mataimakin Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya dira sakateriyar PDP ta ƙasa da ke Abuja ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu, 2024
  • Philip Shaibu ya buƙaci a ba shi satifiket na shaidar zama ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar PDP a zaben jihar Edo mai zuwa
  • Ya ce ya samu labarin cewa Ighodalo ya zo ya karɓi satifiket amma ba zai haƙura ba sai kotu ta raba gardama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya isa sakatariyar jam'iyyar PDP ta kasa da ke birnin tarayya Abuja.

Daga isa sakateriyar, Mista Shaibu ya nemi a ba shi takardar lashe zaben fidda gwani na ɗan takarar gwamnan a inuwar PDP a zaben jihar Edo da ke tafe.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Mataimakin gwamnan PDP ya bankado wata sabuwar makarkashiya da aka shirya masa

Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu.
Mataimakin Gwamnan Edo Ya Dira Hedkwatar PDP ta Kasa Kan Abu 1 Hoto: Mr Philip Shaibu
Asali: Twitter

A rahoton Vanguard, mataimakin gwamnan ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yau ne ranar da aka ware domin karbar takardar shaidar samun nasara ga wanda ya lashe zaben fidda gwani. Na fahimci wani ya zo jiya kuma an ba shi, to kotu za ta yanke hukunci."

An samu ƴan takara biyu a PDP

An bayyana Shaibu a matsayin wanda ya lashe tikitin takarar gwamnan jihar a inuwar PDP a zaben tsagi ɗaya yayin da Asue Ighodalo ya lashe asalin zaben fidda gwani.

Duk da cewa PDP ta gabatar da takardar shaidar lashe zaɓe ga Ighodalo, Shaibu ya je sakatariyar jam’iyyar a ranar Laraba kuma ya nemi a ba shi satifiket.

Mataimakin gwamnan ya jaddada cewa shi ne ya lashe zaɓen fidda ɗan takarar da aka yi, don haka shi za a ba takardar shaida, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Atiku ya tsufa ba zai tsaya takarar shugaban ƙasa a zaben 2027? An fayyace gaskiya

Wanene halastaccen ɗan takarar PDP a Edo?

Kafin wannan rana da aka ganshi a sakateriyar PDP, mataimakin gwamnan jihar Edo ya tabbatar da cewa shi ne sahihin dan takarar jam’iyyar a zaɓe mai zuwa.

Ya kuma yi iƙirarin cewa Ighodalo bai da gogewar sanin tushen siyasa ba inda ake tattara magoya baya kamar yadda ya sani ba.

Shaibu ya ce:

“Zabin da ya rage masu shi ne kada PDP ta je ta yi jayayya da takarata, idan suka yi haka kuma PDP za ta rasa jihar Edo.
"Mutanen Edo ba sa ƙaunar Asue Ighodalo ya zama gwamnan jiharsu saboda shi ba dan gida ba ne da suka sani."

Ministan Tinubu ya sha madarar yabo

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya keɓance ministan harkokin cikin gida, ya yaba masa bisa sauye-sauyen da ya kawo wanda ya rage fushin ƴan Najeriya.

Shugaban ƙasar ya ce ya ji da kunnensa yadda Tunji-Ojo ke shan yabo daga ƴan Najeriya, inda ya ce hakan ya fara ɗaga martabar ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel