Wata Sabuwar Zanga-Zanga Ta Barke a Sakatariyar Jam’iyyar APC Kan Wani Dalili 1 Tak

Wata Sabuwar Zanga-Zanga Ta Barke a Sakatariyar Jam’iyyar APC Kan Wani Dalili 1 Tak

  • Magoya bayan ɗan takarar gwamnan jihar Edo, Dennis Idahosa sun gudanar da zanga-zanga a babbar sakatariyar jam'iyyar APC da ke Abuja
  • Masu zanga-zangar sun nemi Abdullahi Umar Ganduje da ya rushe zaben fidda gwani da aka sake yi a jihar wanda ya ba Okpebola nasara
  • A cewar masu zanga-zangar, an tafka kura-kurai a zaben, kuma an soke zaɓen farko ne kawai don a nuna Okpebola jam'iyyar ke so ba Idahosa ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Masu zanga-zangar maza da mata a ranar Litinin, sun mamaye hedikwatar jam’iyyar All Progressives Congress ta kasa dake babban birnin tarayya, Abuja.

Sun gudanar da zanga-zangar ne domin nuna rashin jin dadinsu kan sakamakon zaben fidda gwani na gwamna da jam’iyyar ta kammala a jihar Edo.

Kara karanta wannan

An yi garkuwa da shaidun zaben gwamnan Kogi a harabar kotun Abuja

Masu zanga-zangar na goyon bayan Dennis Idahosa
Masu zanga-zangar na goyon bayan Dennis Idahosa, wanda ya sha kaye a zaben fidda gwanin. Hoto: MobilePunch
Asali: UGC

Sanata Monday Okpebolo ne ya lashe zaben fidda gwani da jam'iyyar ta gudanar domin fuskantar zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar 21 ga Satumba, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu zanga-zangar na goyon bayan Dennis Idahosa

The Punch ta rahoto cewa masu zanga-zangar, wadanda ke goyon bayan Dennis Idahosa, daya daga cikin ’yan takara 11 da suka sha kaye, sun yi zargin cewa zaben fidda gwani na cike da kura-kurai.

Sun tare babbar kofar sakatariyar jam’iyyar, tare da bukatar ganawa da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, domin neman a yi musu adalci.

Yayin da suke daga kwalaye daban-daban na zanga-zangar, sun yi zargin cewa ba a bi tsarin mulkin jam’iyyar ba wajen gudanar da zaben fidda gwani na jihar.

Bukatar masu zanga-zangar ga jam'iyyar APC

Sannan sun yi kira ga kwamitin ayyuka na kasa na jam'iyyar da ya dawo da zaben fidda gwani na farko da aka yi aranar 17 ga watan Fabrairu, kamar yadda Sahara Repoters ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Kwankwaso ya magantu kan nasarar malamin addini a matsayin dan takarar jam'iyyar NNPP

A zaben ne aka ayyana Idahosa da wasu ’yan takara biyu a matsayin wadanda suka lashe zaben, lamarin da ya tilasta wa shugabannin jam’iyyar bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.

Sai dai magoya bayan Idahosa sun yi iƙirarin cewa an nemi a sake zaɓen ne kawai domin nuna goyon baya ga Okpebolo, wanda aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka sake.

Masu zanga-zaga sun mamaye majalisar dokokin tarayya

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa masu zanga-zaga daga ƙungiyar ƴan ƙwadago (NLC) sun mamaye ginin majalisar dokokin tarayya a ci gaba da zanga-zangar adawa da tsadar abinci.

Joe Ajaero, shugaban kungiyar NLC na kasa ya yi nuni da cewa sun isa ginin majalisar ne don isar da kokensu ga shugaban majalisa, Akpabio

Asali: Legit.ng

Online view pixel